2023: Jam'iyyar PDP Ta Fadi Wanda Atiku Zai Mika Wa Mulki Bayan Gama Wa'adinsa
- Jam’iyyar PDP ta yiwa mutanen yankin kudu maso gabashin kasar alkawarin cewa dan Igbo zata baiwa mulki da zaran Atiku Abubakar ya kammala wa’adinsa
- Mataimakin daraktan labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Uloka Chibuike ne ya fadi hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar
- A cewar Chibuike, Inyamurai za su iya yarda da Atiku saboda ya aikata irin haka a baya
Anambra - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa hanya guda da kabilar Igbo za ta samu shugabancin kasar nan shine su marawa takarar shugabancin Alhaji Atiku Abubvakar baya a 2023, jaridar Punch ta rahoto.
Jam’iyyar ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya tabbatarwa da mutanen kudu maso gabas cewa ana iya damka amana a hannunsa, tana mai cewa babu wata kabila a Najeriya da ta yarda da Ndigbo sannan ta dauke su a matsayin abokan arziki kai tsaye sama da Atiku.
Mataimakin daraktan watsa labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Mista Uloka Chibuike, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ga manema labarai a Awka a ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba.
A cewar Chibuike, yan kabilar Igbo na da babban aiki na marawa Atiku baya a zaben shugaban kasa na 2023 saboda ya dauki alkawarin sauya fasalin lamuran Najeriya ta yadda zai amfani yankin kudu maso gabas da kuma tabbatar da ganin cewa magajinsa ya fito daga yankin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce yankin zai fi samun alfanu ta hanyar yin hadaka da arewa, jaridar TheCable ta rahoto
Ya ce:
“Za mu fi cin amfani ta hanyar yin hadaka da arewa fiye da sauran yanki a kasar nan. Atiku ya tabbatarwa dan Igbo cewa shi dan amana ne. Babu wata kabila a Najeriya da ta yarda da Inyamuri sannan ta mayar da shi aboki kai tsaye a bangaren ci gaba, sai Atiku.
“A 2007, ya yi watsi da duk wata hatsaniya, ya zabi dan Igbo daga jihar Anambra wato Sata Ben Ndi Obi don ya zama abokin takararsa.
“Duk da adawar da wasu dama suka nuna, ya zabi Mista Peter Obi a matsayin abokin takararsa a 2019 don tabbatar da dangantakarsa da yan Igbo.
“Bugu da kari, duk da haramcin da Ohanaeze ta sanya kan yan siyasar Igbo na amincewa da kujerar mataimakin shugaban kasa a 2023, Atiku ya sake zabar dan Igbo a matsayin abokin takara a 2023, yana mai alkawarin mika mulki gad an Igbo bayan wa’adin mulkinsa.
“Atiku ya sha alwashin sake fasalin Najeriya ta yadda zata amfani yan Igbo sannan ya tabbatar da ganin cewa magajinsa ya fito daga yankin. Wannan ba wai alkawari bane kawai, ya sha nuna cewa shi baya magana biyu. Yayin da saura ke ci gaba da yiwa yan Igbo rikon goriba a hannun kuturu, Atiku ya yi alkawarin kula da mu cikin mutunci.”
A wani labarin kuma, Legit.ng ta kawo a baya cewa wasu mutane da ake zaton yan bangar siyasa ne sun farmaki tawagar Atiku Abubakar a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Lamarin ya afku a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba inda mutane suka nemi mafaka yayin da karar harbi ya dungi tashi a wajen.
Asali: Legit.ng