Shugaban Yakin Neman Zaben Atiku Zai 'Ajiye' Aiki Saboda Karancin Kudin Kamfe

Shugaban Yakin Neman Zaben Atiku Zai 'Ajiye' Aiki Saboda Karancin Kudin Kamfe

  • Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya rasa yadda zai yi da yakin neman zaben Atiku Abubakar
  • Na kusa da Mai girma Udom Emmanuel sun ce ana kukan karancin kudin yi wa Atiku kamfe a 2023
  • Takarar tsohon mataimakin shugaban kasar tana fuskantar kalubale saboda yadda aka matse aljihu

Akwa Ibom - Jita-jita na yawo cewa Gwamna Udom Emmanuel yana barazanar murabus a matsayin shugaban kwamitin takarar Atiku Abubakar.

Jaridar Sun tace Mai girma Udom Emmanuel yana maganar zai ajiye kujerar shugaban kwamitin yakin zabe na PCC idan ba a saki kudin kamfe ba.

Amma da aka tuntubi Kwamishinan yada labarai da dabaru na Akwa Ibom, Ini Ememobong, ya shaida cewa bai san da wannan maganar da ke yawo ba.

Ini Ememobong yace Mai gidansa ba zai yi wa Atiku Abubakar barazana kan batun kamfe ba. Sahara Reporters ta tabbatar da wannan a ranar Talatar nan.

Kara karanta wannan

Gwamna Lalong Ya Shigar Da Ali Nuhu, Duniyar Kannywood Yakin Neman Zaben Tinubu/Shettima

Ba za ayi haka ba - Kwamishina

“Gwamna dattijo ne, ba ya yin barazana, yana tattaunawa ne. Mutum ne mai bin abubuwa a hankali a duk inda ya samu kan shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saboda haka mun san da cewa yana kokarin ganin an yi sulhu kuma an samu zaman lafiya domin taimakawa jam’iyya tayi nasara.

- Ini Ememobong

Atiku Abubakar
Alhaji Atiku Abubakar a Amurka Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Akwai kanshin gaskiya

Amma duk da musanya batun da Kwamishinan ya yi, wata majiya daga gidan gwamnatin Akwa Ibom ta tabbatarwa Jaridar Daily Sun wannan magana.

Wasu na-kusa da Mai girma gwamnan sun ce ran sa ya baci kan yadda ‘dan takaran shugaban kasar ya ki fito da kudi domin yi masa kamfe a Akwa Ibom.

Hadiman Gwamnan sun nuna jam’iyyar PDP tana fuskantar barazana a zaben shugaban kasa, don haka ake bukatar kudi domin nasarar Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

Babu kudin yakin zabe a 2023?

“A halin yanzu gwamnan mu yace ba zai kashe ko sisi daga cikin Baitul-malin jiharsa domin yakin neman zaben shugaban kasa ba.
Ba mu da isasshen kudin da za muyi yakin neman takarar majalisa. Yace zai fi masa sauki ya yi murabus da ya rasa abin da zai yi.

Majiyar take cewa shugaban kwamitin na kamfe yana so ya taimakawa Atiku, amma babu abin da zai iya yi masa yanzu saboda karancin kudi da ake da shi.

“Babu hamayya a jihar Zamfara"

Jam’iyyar APC ta ci zabe ta gama a jihar Zamfara, ba a maganar ‘Yan adawa. An ji labari Kabiru Garba Marafa ya fadawa Bola Tinubu wannan.

Tsohon Sanatan wanda yake jagorantar yakin neman zaben Bola Tinubu yana neman a jawo har ‘Dan takaran Gwamna a APC, ya dawo APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel