Gwamnan Bauchi Ya Fusata da Atiku, Ya Aike Masa da Muhimmin Sako

Gwamnan Bauchi Ya Fusata da Atiku, Ya Aike Masa da Muhimmin Sako

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya fusata ta yanayin yadda aka ware shi a tafiyar Kamfen Atiku Abubakar
  • Gwamnan, a wata wasiƙa da ya aika wa uwar jam'iyyar PDP ya nemi ɗan takarar shugaban ƙasa ya gaggauta ba shi hakuri
  • Sabbin rigingimu na ƙara kunno kai a babbar jam'iyyar adawa PDP duk da ba'a warware rikici da tsagin Wike ba

Bauchi - Sabbin matsaloli na ƙara kunno kai a babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP, bayan gwamnonin G-5, ƙarƙashin gwamnan Ribas, Nyesom Wike, gwamna Bauchi, Bala Muhammed, yace ba'a kyauta masa ba.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnan ya ce ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya maida shi saniyar ware a kwamitin kamfe (PCC).

Bala Muhammed na Bauchi.
Gwamnan Bauchi Ya Fusata da Atiku, Ya Aike Masa da Muhimmin Sako Hoto: Senator Bala Muhammed
Asali: Facebook

Da yake nuna fushinsa, Muhammed ya yi zargin cewa Atiku ya yi barazanar hukunta shi sakamakon gogayya da shi a zaɓen fidda gwanin PDP da ya gudana a watan Mayu, Sahara Reporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Rikicin Wike Somin Taɓi Ne' Tsohon Gwamnan PDP Ya Hango Babbar Matsala Ga PDP, Atiku Gabanin 2023

Idan baku manta ba, gwamna Muhammed, ya gwabza da Atiku a tseren lashe tikitin PDP na kujera lamba ɗaya a Najeriya, amma tare da wasu 'yan takara 12 sun sha kasa a zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammed, wanda aka naɗa mataimakin shugaban kwamitin kamfen shugaban ƙasa, ya nuna fushinsa ne a wata wasiƙa mai lambar asali GH/OFF/09/V.I da kwanan watan 3 ga Nuwamba.

Wasiƙar da ya aike wa shugaban jam'iyya, Iyorchia Ayu, na ɗauke da sa hannun Muhammed, mataimakinsa, Bala Tela, kakakin majalisar dokokkn Bauchi, Abubakar Suleiman, shugaban PDP na jiha, Hamza Akuyam, da wasu 30.

Ƙorafin da gwamnan ya rubuta a wasikar

"An watsar da ni a gangamin yakin neman zaɓen da PCC ya shirya a Kaduna, wanda aka zauna da ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki da manyan arewa da suka wakilci ƙungiyoyin daban-daban," inji shi.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa a APC, Wani Babban Jigo da Wasu Shugabanni Sun Ayyana Goyom Baya Ga Ɗan Takarar PDP a 2023

Bugu da ƙari, Muhammed ya yi zargin cewa wasu 'yan koran siyasa a Bauchi sun tasa shi a gaba, waɗanda a ɓoye ko a fili, tsohon mataimakin shugaban ƙasan ke goya musu baya.

"Yayin da Atiku da yan koransa ke kokarin hukunta ni saboda kawai na yi gogayya da shi a zaɓen fidda gwanin PDP, su mutanen da suka zagaye Atiku masu ikirarin suke naɗa sarki na kokarin mun zagon kasa."
"Saboda na ƙi miƙa wuya ga son ransu. Tawagar karshe dake fafutukar ganin bayan Bala, 'Bala Must Go' su ne waɗanda tarihinsu ya goge sakamakon dumɓin nasarori da ayyukan alherin gwamnatin PDP a Bauchi."

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta sake gamuwa da cikas yayin da manyan jiga-jigai sama da 300 suka tattara zuwa APC

Rahotanni daga jihar Ondo dake kudu maso yammacin Najeriya sun ce aƙalla masu faɗa aji na PDP 300 ne suka yaga laima, kana suka kom a APC.

Kara karanta wannan

Abubuwa Sun Sukurkucewa PDP, Gwamnan Arewa Yana Barazanar Yin Watsi da Atiku

Mutanen waɗanda suka hito daga yankin ƙaramar hukumar Idanre a Ondo, sun ce ba zasu iya zama a jam'iyyar da ta gaza samar da zaman lafiya a cikinta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel