Hotuna: Gwamna Wike Ya Jagoranci Tawagar Gwamnonin PDP 5 Sun Dira Benuwai

Hotuna: Gwamna Wike Ya Jagoranci Tawagar Gwamnonin PDP 5 Sun Dira Benuwai

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jagoranci takwarorinsa na G-5 zuwa jihar Benuwai dake arewacin Najeriya
  • Wasu hotuna da suka bayyana sun nuna yadda gwamna Samuel Ortom ya tarbe su hannu bibbiyu cikin farin ciki
  • Tun bayan zaben fidda gwanin PDP ake kai ruwa rana a jam'iyyar musamman tsakanin Wike da Iyorchia Ayu

Benue - Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, ya jagorancin fustattun gwamnonin jam'iyyar PDP zuwa jihar Benuwai dake arewa ta tsakiya a Najeriya, inda gwamna Samuel Ortom ya tarbesu cikin farin ciki.

Baya ga gwamna Wike da Ortom, gwamnonin da ke cikin tawagar G-5 sun haɗa da, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na jihar Abiya da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

Tawagar G5.
Hotuna: Gwamna Wike Ya Jagoranci Tawagar Gwamnonin PDP 5 Sun Dira Benuwai Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto muku cewa gwamnonin da dukkanin masu goya musu baya sun tsame hannu daga kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi

Bugu da ƙari sun kafa sharɗin murabus ɗin shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, a matsayin hanya ɗaya tilo ta samun zaman lafiya a PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ɗan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, a wata hira da kafar VOA Hausa yace sauya ahugabancin PDP a halin yanzu ba abu ne mai yuwuwa ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasan yace tuni ya tsallake daga matakin rikicin ciki gida ya ci gaba da harkokin tunkarar babban zaɓe mai zuwa.

Wasu Hotunan gwamnonin a jihar Benuwai

Gwamna Ortom.
Hotuna: Gwamna Wike Ya Jagoranci Tawagar Gwamnonin PDP 5 Sun Dira Benuwai Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Tawagar Wike a Benuwai.
Hotuna: Gwamna Wike Ya Jagoranci Tawagar Gwamnonin PDP 5 Sun Dira Benuwai Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wike da Ortom.
Hotuna: Gwamna Wike Ya Jagoranci Tawagar Gwamnonin PDP 5 Sun Dira Benuwai Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wike da Ortom.
Hotuna: Gwamna Wike Ya Jagoranci Tawagar Gwamnonin PDP 5 Sun Dira Benuwai Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Tun bayan kammala zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP aka nemi zaman lfiyar cikin gida aka rasa a babbar jam'uyyar hamayya.

Gwamna Wike, jagoran mambobin da suka fusata da aakamakon zaɓen, sun ce ba zai yuwu ɗan takarar da shugaban jam'iyya su fito daga yanki ɗaya ba.

Kara karanta wannan

'Mun Matsa Gaba' Atiku Ya Magantu Kan Yuwuwar Sasantawa da Su Wike Gabanin 2023

Bisa haka suka ci gaba da kiraye-kirayen shugaban PDP na ƙasa ya sauka daga muƙaminsa domin ɗan kudu ya maye gurbinsa.

A wani labarin kuma Atiku Ya Magantu Kan Yuwuwar Sasantawa da Su Wike Gabanin 2023, yace ya daina damuwa da rikicin PDP

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace ba zai yuwu a sauya shugabancin jam'iyyar PDP ba a yanzu.

Da yake tsokaci kan rikinsu da gwamnonin tsagin Wike, Atiku yace tuni ya daina damuwa kan batun ya matsa gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel