Sarakuna 17 Sun Yi Watsi da Atiku, Sun Karyata Batun Goyon Bayan Takararsa

Sarakuna 17 Sun Yi Watsi da Atiku, Sun Karyata Batun Goyon Bayan Takararsa

  • Sarakunan da ke mulki a kasar Idemili sun fitar da sabon jawabi a kan goyon bayan wani ‘dan takara
  • Kamar yadda suka bayyana ta bakin kungiyarsu, Sarakunan gargajiyar sun nesanta kansu daga PDP
  • Rahotanni na yawo cewa Atiku Abubakar ya samu goyon bayansu, ta tabbata hakan ba gaskiya ba ne

Anambra - A baya an rahoto cewa Sarakunan gargajiya 17 da ke sarauta a garuruwan Idemili a jihar Anambra, su na tare da Atiku Abubakar a 2023.

A wancan lokaci an ji cewa ‘Dan takaran shugaban kasar na PDP da Ifeanyi Okowa sun ci albarkacin Farfesa Obiora Okonkwo a wajen Sarakunan.

Kwatsam sai ga labari daga This Day, an rahoto Sarakunan na karamar hukumar Kudu da Arewacin Idemili su na nesanta kansu da tafiyar PDP.

Kara karanta wannan

Ba Zamu Yarda Wani Dan Arewa Ya Gaji Buhari Ba: Kungiyoyin Kasar Yarbawa

Masu kasar sun fitar da jawabi ta bakin shugabannin kungiyarsu; Igwe Chuma Agbala da Igwe Nick Obi, suka yi karin bayani a kan matsayarsu.

Igwe Agbala da Igwe Obi sun yi karin bayani

A jawabin da suka fitar, Sarakunan sun ce Dr. Obiora Okonkwo ya kawo masu ziyara ne kurum, ya kuma yi masu bayani PDP na neman ya yi mata aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Obiora Okonkwo yana cikin Darektocin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da Atiku Abubakar yake yi a karkashin jam'iyyar PDP a 2023.

Atiku
Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

"Rahoto ko bayanin da yake yawo a gidajen yada labarai na goyon bayan ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba gaskiya ba ne.
Hakikanin abin da ya faru shi ne Sarakunan gargajiyan karamar hukumar Idemili ta Arewa da Kudu sun yi zamansu na duk wata uku.
An yi taro a hedikwatar Idemili ta Arewa Ogidi, sai Cif Obiora Okonkwo ya zo ya shaida yana cikin jagororin kamfen PDP a Anambra.

Kara karanta wannan

Gida Bai Koshi Ba: Kungiyar Yarbawa Ta Bayyana Wanda Take So Ya Gaje Buhari Tsakanin Obi Da Tinubu

Iyakarta kenan, babu wata mubaya’a da aka yi wa wata jam’iyya ko wani mai takara."

- Igwe Chuma Agbala da Igwe Nick Obi

Sun ta rahoto Sarakunan su na cewa a matsayinsu, babu ruwansu da jam’iyya a siyasa, suka ce su iyayen ‘yan takara ne, ba za su goyi bayan wani ba.

Atiku Abubakar zai gwabza da Bola Tinubu, Peter Obi da su Rabiu Kwankwaso a 2023.

Rikici a APC a Kano

Kun samu labari rigima ta shiga tsakanin jagororin jam’iyyar APC da ake je yin taro a gidan Mai girma mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna.

Bayan abin da ya faru, Alhassan Doguwa da ya yi rikici da ‘Dan takarar Mataimakin Gwamna, Murtala Sule Garo yace abokin fadan ne ya nemi rigima da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng