Gida Bai Koshi Ba: Kungiyar Yarbawa Ta Bayyana Wanda Take So Ya Gaje Buhari Tsakanin Obi Da Tinubu

Gida Bai Koshi Ba: Kungiyar Yarbawa Ta Bayyana Wanda Take So Ya Gaje Buhari Tsakanin Obi Da Tinubu

  • Kungiyar kare muradun Yarbawata ta Afenifere ta jadadda wanda take goyon baya a babban zaben shugaban kasa mai zuwa
  • Pa Reuben Fasoranti, shugaban kungiyar na kasa yace Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC shine zabinsu
  • Fasoranti ya ce ko kadan basa goyon bayan dan takarar Labour Party, Peter Obi, domin bai da gurbi a zukatansu

Shugaban kungiyar kare muradun Yarbawa ta Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, ya jadadda cewa shi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lamunce mawa.

Pa Fasoranti, wanda ya ce har gobe shine shugaban Afenifere, ya ce kungiyar bata tsayar da dan takarar jam’iyyar Labour Party, Mista Obi ba, jaridar The Nation ta rahoto.

Tinubu da shugabannin Afenifere
Gida Bai Koshi Ba: Kungiyar Yarbawa Ta Bayyana Wanda Take Goyon Bayan Ya Gaje Buhari Tsakanin Obi Da Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A wani bidiyo da ya yadu, an gano dattijon mai shekaru 97 yana nuna cewa yana sane da abubuwan da suka faru a kungiyar ta Afenifere.

Kara karanta wannan

Tinubu: Abin da Buhari Ya Fada Mani Yayin da Na Nemi Ya Zakulo Mani Mataimakina

Rahoton ya nakalto Fasoranti yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Har yanzu nine shugaban Afenifere. Afenifere bata tsayar da Obi ba, Jagaban (Bola Ahmed Tinubu) ne dan takararmu na shugaban kasa.
“Kamar yadda kuke gani, lamuncewa da karbuwar da ya samu. Kun ga abun da ya faru lokacin da Tinubu ya zo don ganawa da ni a Akure. Kafofin watsa labarai sun dauki gaba daya abun da ya faru.
“Adebanjo bai da ikon yi mun gargadi don kada na tarbi Tinubu. Shin zai iya yin hakan cikin nasara?
“Abun da ya faru shine cewa Adebanjo ya kama matsaya nima kuma na kama matsaya. Ban kira shi kuma shima bai kira ni ba. Bamu yi magana game da ziyarar ba.
“Kamar yadda kuka gani, Jagaban ya samu karbuwa kuma mun amince da shi. Obi bai da matsayi a zukatanmu ko kadan."

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Babbar Kungiyar Yarbawa da Gwamnan PDP

Daga Karshe Bola Tinubu Ya Amsa Bukatar Yan Najeriya, Ya fadi Hanyoyin Arzikinsa

A wani labarin, mun ji cewa bayan yan Najeriya da dama a fadin duniya sun nemi jin ta bakinsa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya magantu kan tushen arzikinsa.

Yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin kungiyar NAPOC a Abuja, Tinubu ya bayyana cewa yana da gidajen gas biyu a birnin Landan, jaridar The Nation ta rahoto.

A cewar tsohon gwamnan na jihar Lagas, matarsa Remi ita ce ke kula da gidajen man wanda daga bisani ya siyar da su domin daukar nauyin rusasshiyar jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO).

Asali: Legit.ng

Online view pixel