Dan Takarar Sanatan APC a Kogi, Da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma Jam'iyyar ADC

Dan Takarar Sanatan APC a Kogi, Da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma Jam'iyyar ADC

  • Oni Christopher Tosin da dubban magoya bayansa sun sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa ta ADC
  • Tosin ya ce ya bar APC ne saboda bata da tsari, kuma romon da yake tsammani na dimokradiyya ba ya samu a cikinta
  • Madam Abusi Edumare, jigon siyasar yankin Yagba a jihar ta bayyana komawa jam'iyyar ADC daga jam'iyyar APC

Jihar Kogi - Dan takarar sanata a jam'iyyar APC a jihar Kogi, Oni Christopher Tosin da dimbin masoyansa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC.

Wannan ya faru ne a wani bikin da ya samu halartar jiga-jigai irinsu Leke Abejide, mamban majalisa mai waliltar Yagba a majalisar kasa da aka gudanar a Egbe, karamar hukumar Yagba ta Yamma a jihar ta Kogi.

Jam'iyyar APC ta yi rashi, jiga-jiganta sun sauya sheka zuwa ADC
Dan takarar Sanatan APC a Kogi, da wasu jiga-jigai sun koma ADC | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Leke Abejide ya bayyana jin dadinsa da samun Tosin a matsayin mamban jam'iyya, kuma a cewarsa, jam'iyyar ta yi babban kamu da samunsa, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya samu nakasu a Sokoto, manyan jiga-jigai sun koma APC

Bayan karbarsa hannun biyu zuwa ADC, ya kuma bayyana shi a matsayin babban kayan aikin ciyar da jam'iyyar gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilin da yasa Tosin ya bar APC ya koma ADC

Tosin ya shaidawa ilahirin jama'a cewa, ya bar jam'iyyar APC ne saboda rashin dimokradiyyar cikin gida da kuma rashin shugabanci na gari a mazabarsu dake a jihar Kogi.

Hakazalika, ya koka tare da ganin gazawar jam'iyyar wajen tsara yadda za ta lashe zabe mai zuwa a 2023 a jihar Kogi, musamman dai mazabar tasu.

Madam Abusi Edumare, jigon siyasa a karamar hukumar Yagba ta Yamma ita ma ta bayyana barin jam'iyyar mai ci a jihar tare da jamewa a jam'iyyar ADC.

An samu wasu jiga-jigan APC na yankin Yagba da dama da suka bayyana ficewarsu daga jam'iyyar tare da kama tafiyar jam'iyyar ADC.

Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP, Atiku Ya Nada Ibrahim Zango a Matsayin Babban Sakatare

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nada Ibrahim Zango a matsayin babban sakatarensa.

Nadin Zango na zuwa ne a cikin wata wasika mai dauke sa hannun dan takarar na PDP, kamar yadda Daily Nigerian tace ta samo.

Zango, wanda asalinsa dan jihar Katsina ne ya kasance fitaccen ma'aikacin gwamnati da ya yiwa kasa hidima a ciki da kasashen waje, ciki har a Burtaniya da Saudiyya da dai sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel