2023: Mambobin APC Sama da 200 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Yankin Wani Gwamnan Arewa

2023: Mambobin APC Sama da 200 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Yankin Wani Gwamnan Arewa

  • Gabannin zaben 2023, jam'iyyar APC ta rasa daruruwan mambobinta a yankin Kofar Kola da ke Birnin Kebbi, babbar birnin jihar Kebbi
  • Masu sauya shekar da suka hada da maza 134 da mata 84 sun koma jam'iyyar PDP mai adawa a kasar
  • Tsoffin mambobin na APC sun samu kyakkyawar tarba daga dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar, Janar Aminu Bande mai ritaya

Kebbi - Akalla mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 216 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a yankin Kofar Kola da ke Birnin Kebbi, babbar birnin jihar Kebbi.

Jam’iyyar APC na da karfi sosai a garin Kofar Kola saboda kasancewarsa yankin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu.

APC da PDP
2023: Mambobin APC Sama da 200 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Yankin Wani Gwamnan Arewa Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Wadanda suka sauya shekar zuwa PDP da suka hada da maza 134 da mata 84 sun kasance mambobin jam’iyyar mai mulki a yanki.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Na PDP Ya Rasa Magoya Bayansa Fiye Da 5,000, Sun Koma APC

Manyan shahararrun yan siyasa a cikinsu sun hada da Alhaji Atiku Bandado, Alhaji Gwandu Mai Kifi, Alhaji Yahaya Lele, tsohon hadimin gwamnan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai kuma Alhaji A.M. BK, wanda ya kasance tsohon shugaban kwalejin ilimi na Adamu Augue da ke jihar.

Masu sauya shekar sun samu tarba daga dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar, Janar Aminu Bande mai ritaya.

Sauran wadanda suka yi masu lale marhaban sun hada da darakta janar na kwamitin yakin neman zaben gwamnan, Alhaji Abubakar Shehu, sakataren labaran jam’iyyar, Alhaji Sani Dododo da kuma sauran jiga-jigan PDP a jihar.

Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

A wani labarin, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya magantu a kan yiwuwar hadakarsu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso gabannin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Anambra da Jihohi 7 da Peter Obi Zai Iya Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

Daily Trust ta rahoto cewa Shettima ya bayyana cewa shi da kansa zai nemi Kwankwaso a daidai lokacin da ya kamata.

Tsohon gwamnan na jihar Borno wanda ke gabatar da jawabi a taron kungiyar limaman birnin tarayya Abuja, yana barkwanci ne da tsohon dan majalisar wakilai, Garba Ibrahim Muhammed, wanda ya wakilci Sanata Kwankwaso a taron.

Shettima ya ce:

“Na sha alwashin ba zan taba muzanta Sanata Rabiu Kwankwaso ba har a gama zabe mai zuwa. Shi din shugaba ne nagari, kuma da izinin Allah, za mu zauna sannan mu fahimci junanmu a lokacin da ya dace nan kusa.
“Wadanda ke shirin raba kan kasar nan ba za su cimma nasara ba, kuma saboda haka, ya zama dole mu lamunci junanmu sannan mu sadaukar da abubuwa.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel