Rikicin PDP: Tsagin Gwamna Wike Sun Sake Huro Wuta, Suna Neman a Dake Zaman NEC

Rikicin PDP: Tsagin Gwamna Wike Sun Sake Huro Wuta, Suna Neman a Dake Zaman NEC

  • Zaman lafiya na ci gaba da ƙauracewa jam'uyyar PDP yayin da masu mara wa Wike baya suka sake huro wuta kan Ayu
  • Wasu mambobin NWC da shugabannin PDP na jihohi sun fara yunkurin ganin an kira sabon taron NEC
  • Yan takarar gwamna a inuwar PDP musamman daga kudu sun ce ba su san yadda za'a siyar da PDP a yankinsu ba

Abuja - Rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP ya sake buɗe sabon shafi yayin da tsagin masu goyon bayan gwamnan Ribas, Nyesom Wike, suka matsa lamba kan a kira taron majalisar zartasawa (NEC) ta ƙasa.

Vanguard ta gano cewa wasu makusantan Wike a cikin kwamitin ayyuka (NWC) da wasu shugabannin PDP a jihohi ne ke faɗi tashin ganin an sake kiran taron NEC.

Kara karanta wannan

2023: Rikicin PDP Ya Kara Dagulewa, Shugaban Jam'iyyar Ya Yi Fatali da Shawarin Dattawa

Ayu da gwamna Wike.
Rikicin PDP: Tsagin Gwamna Wike Sun Sake Huro Wuta, Suna Neman a Dake Zaman NEC Hoto: vanguard
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa sun hura wannan wuta ne a yunkurinsu na tattara kayan shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya bar Ofishinsa. Idan baku manta ba Ayu yace ba wanda ya isa ya tsige shi.

Jiga-jigan PDP, makusantan gwamna Wike da wasu mambobi da basu gamsu da tsarin tafiyar da jam'iyyar ba ne suka sake yunƙurowa da nufin tsige Ayu daga muƙaminsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani rahoto ya nuna cewa 'yan takarar gwamna a wasu jihohi karkashin PDP na shirin fara kira ga Ayu ya yi murabus kuma suna goyon bayan yunkurin sake zaman NEC.

An hakaito wani ɗan takarar gwamna daga shiyyar kudu maso gabashin Najeriya na cewa, "Mafi yawan yan takarar PDP musamman daga kudu sun damu da halin da jam'iyya ke ciki."

"Kamar yadda su Wike suka nuna lokuta da dama, ta ya Atiku da Ayu zasu ja hankalin 'yan kudu su zaɓi PDP, ta ya zamu tallata musu su zabi jam'iyyar da ke nuna kudu ba'a bakin komai take ba?"

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗaliban Fitacciyar Jami'a A Najeriya

"Kuma mu a matsayin yan takara masu burin lashe zaɓe, ba zamu iya gum da bakinmu ba kan wannan batun. Mun gaya wa manyan mu su sanya jam'iyya saman kowa."
"Amma ta bayyana babu wanda ke da ra'ayin shiga jirginmu, don haka mun cimma matsayar fuskantar matsalar da kanmu ta hanyar fitowa duniya mu yi magana."

Ya nemi Ayu ya hakura ya yi murabus

Mai fatan zama gwamna a 2023 ya ƙara da cewa kiraye-kirayen murabus ɗin shugaban PDP ƙaruwa yake kullun, ya roki Ayu ya duba muradun jam'iyya ya maida wukarsa kube.

Yace, "Ba dalilin da zai ƙi murabus ko dan muradan jam'iyya, shi ubanmu ne kuma ya kamata ya ɗauki goben siyasarmu da muhimmanci fiye da kowa."

A wani labarin kuma Shettima Ya Yi Karin Haske Kan Yuwuwar Hada Kai Tsakanin Tinubu da Kwankwaso a Zaben 2023

Gabannin babban zaben 2023, Sanata Kashim Shettima ya yi karin haske kan yiwuwar hadewarsu da dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

"Dalilin Da Yasa Cikin Sauki Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasan 2023"

Shettima wanda shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC ya ce za su zauna su fahimci juna da tsohon gwamnan na jihar Kano a lokacin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel