Ka yi kadan: Gwamna Wike Ya Aikawa Shugaban Jam’iyyar PDP Sabon Raddi
- Gwamna Nyesom Wike ya maida martani ga jawabin da aka ji shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya yi
- Iyorchia Ayu ya yi ikirarin zai iya hana mutum takara, amma Wike yace Ayu bai da wannan karfi a doka
- Gwamnan ya kalubalanci shugaban jam’iyyar ya soke takarar wasu daga cikin ‘yan takaran PDP a Ribas
Rivers - Gwamna Nyesom Wike ya maida martani bayan shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu yace zai iya hana wasu shiga takara.
Daily Trust ta rahoto Mai girma Nyesom Wike yana mai kalubalantar Iyorchia Ayu ya hana wani ‘dan takaran jam’iyyar PDP shiga zabe a 2023.
Wike ya zanta da manema labarai a garin Fatakwal, yana yin raddi ga shugaban jam’iyyarsa.
A cewar Gwamnan, babu wanda yake kiran a sauke Ayu daga mukaminsa, sai dai ana neman ya yi murabus saboda Atiku Abubakar ya samu tikiti.
Jawabin Gwamna Nyesom Wike
"Kalaman da suka fito daga bakin shugaban PDP na kasa na hana wani ‘dan takara shiga zabe, abin takaici ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu wanda yace a tsige Sanata Iyorchia Ayu. A tsarin mulkinmu, akwai tsarin karba-karba a jam’iyyun siyasa.
Babu ta yadda shugaban jam’iyya na kasa da kuma ‘dan takarar shugaban kasa za su fito daga wuri daya.
Abin da muke cewa shi ne Ayu ya cika alkawari, ya yi murabus tun da ‘dan takaran shugaban kasa ya fito
Ka zo Ribas idan ka isa
Punch ta rahoto Gwamnan yana cewa idan har shugaban jam’iyyar yana ganin ya na da iko, ya zo jihar Ribas ya hana wani ‘dan takara shiga zabe mai zuwa.
“Ina kalubalantarsa ya zo jihar Ribas, ya hana wani ‘dan takara shiga zabe. Shin ku na so ku ci zabe? Shakka babu Jam’iyya tana cikin tsaka-mai-wuya.
Na kalubalance shi, Ayu ya zo ya hana wani ‘dan takara shiga zabe. Ya san ba zai iya ba, bai da wannan ikon, ya zo Ribas, ina mai kalubalantar shi.
Ana neman murde zabe
Da aka yi hira da shi a gidan talabijin, kun ji labari Buba Galadima ya nemi Muhammadu Buhari yayi hattara domin ‘ya ‘yan APC na shirin magudi.
Injiniya Buba Galadima ya kara nanata rade-radin da ke yawo na cewa wasu na neman yadda za su yi domin a ki yin amfani da BVAS a zabukan 2023
Asali: Legit.ng