2023: Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Ya Rufe Ofishin PDP A Okene, Mutane Sun Yi Martani

2023: Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Ya Rufe Ofishin PDP A Okene, Mutane Sun Yi Martani

  • Hukumomin gwamnati na cigaba yi wa jam'iyyun hamayya matsalin lamba a jihar Kogi gabanin zaben 2023
  • Wasu da ake zargin masu biyayya ga gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello sun rufe ofishin PDP a karamar hukumar Okene
  • Yan Najeriya a dandalin sada zumunta sun riaka sukar gwamnan saboda matakin da ya dauka, suna cewa hakan bai tsarin demokradiyya bane

Okene - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya rufe babban ofishin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar.

A cewar Sahara Reporters, rufe ofishin na cikin shirin na Gwamna Bello don tsayar da kamfen din Natasha Akpoti da ke takarar sanata a jihar.

Yahaya Bello
2023: Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Ya Rufe Ofishin PDP A Okene. Hoto: Gwamnatin Jihar Kogi
Asali: Facebook

Akpoti na takarar kujerar sanata ne a na mazabar Kogi Central a karkashin jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, a 2019.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ba Wa Cocin Katolika Kyautan Naira Miliyan 20 A Wata Jihar Arewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A shekarar 2019, ta yi takarar kujerar gwamna a jihar, ta fafata tare da Bello. A Mayu, Akpoti ta ci zaben fidda gwani na Kogi Central a 2023, za ta fafata da Abubakar Ohere na APC da wasu.

An ambato wata majiya a rahoton ta ce:

"Domin dakile abokan hamayya, Yahaya Bello ya rufe babban ofishin PDP a Kogi Central don hana Natasha Akpoti yin kamfen din sanata. Natasha yar asalin Okene ne kuma nan ne inda ta fi karfi."

Wata majiya da aka ambata a rahoton, ta tabbatar da rufe ofishin, tana mai cewa a baya Yahaya Bello ya yu gargadin cewa zai 'gasa wa PDP aya a hannu' gabanin zabe.

A wasikar da aka tura mata na gargadi mai dauke da sa hannun ciyaman din karamar hukumar Okene, Hon. Abdulrazak M. Yusuf, ya fada wa PDP ta tashi daga ofishin, saboda dalilin tsaro.

Kara karanta wannan

Anambra da Jihohi 7 da Peter Obi Zai Iya Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

Wani sashi na wasikar ya ce:

"A matsayin wani mataki na yin garambawul ga tsaron mu, an baku notis na mako daya ku tashi daga sakatariyar PDP a Okene.
"An dauki wannan matakin ne saboda abin da kwamitin tsaro suka ce kusancin sakatariyar ku wasu muhimman gine-gine kamar; Babban masallacin Ebira da sakatariya wadanda idan aka fara harkokin siyasa zai iya kawo cikas da zaman lafiya a wurin.
"Bari in fayyace cewa kwamitin ba ta dauki wannan matakin don siyasa ba don haka kada a yi masa wannan kallon. Mun gode."

Wasu yan Najeriya sunyi martani kan lamarin

Wasu yan Najeriya a dandalin sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu kan rufe ofishin na PDP a Okene

Vera Okotie a Twitter ta rubuta:

"Matashin gwamna ya da kamata ya zama mai nuna kara da soyayya yana abu kamar fitanannen tsoro."

Charles Akue ya rubuta:

"Duk ya fara ne daga Legas inda suka fara hana jam'iyyun hamayya wurin talla da yi wa kamfanonin talla barazana."

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan PDP mai ba Atiku ciwon kai ya zabo tsohon jigon APC ya zama kwamishinansa

Kenneth Onyebuchi ya rubuta:

"Bisa alamu yana da kyau mu sani daga Yahaya Bello cewa ba dukan waɗanda suka mori dukar 'kuriciya bata hana takara' suka cancanci alfarlmar ba.' Halayen Yahaya Bello tun bayan da ya zama gwamna ba abin alfahari bane. Ayyukansa babban abin takaici ne ga matasa, ya tabbatar da cewa ba dukkan matasa ne suka cancanta ba."

Zaben 2023: Dan Takarar Gwamna Na PDP Ya Rasa Magoya Bayansa Fiye Da 5,000, Sun Koma APC

A wani rahoton, dumbin magoya bayan dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Legas, Abdulazeez Adediran da aka fi sani da Jandor, a ranar Alhamis, sun koma jam'iyyar APC.

Wadanda suka sauya shekan mambobin kungiyar Lagos4Lagos wanda Jandor ya kafa, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel