Anambra da Jihohi 7 da Peter Obi Zai Iya Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

Anambra da Jihohi 7 da Peter Obi Zai Iya Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

  • Takarar Peter Obi a zaben sabon shugaban kasa mai zuwa tana cigaba da motsa siyasar Najeriya
  • Peter Obi ya samu karbuwa musamman a Kudancin Najeriya da wasu jihohi a Arewacin kasar nan
  • Ana hasashen Jam’iyyar Labour Party za ta gwagwiyi kuri’un da Atiku Abubakar ya samu a 2019

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta kawo jihohin da ake tunanin jam’iyyar Labour Party za tayi wa Atiku Abubakar illa a zaben 2023.

1. Anambra

Peter Obi zai iya samun gagarumar galaba a Anambra domin daga jihar ya fito, kuma ya yi gwamna sau biyu, yana da magoya-baya a yankin.

2. Abia

Jihar Abia tana cikin jihohin PDP da suka samu sabani da Atiku Abubakar. Idan ba ayi sulhu ba, Peter Obi zai amfana da wannan baraka.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan PDP 5 Da Sukayi Watsi Da Atiku Suka Koma Bayan Peter Obi

3. Enugu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shi ma Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi yana tare da bangaren Nyesom Wike, zai yi wahala PDP ta maimaita nasarar 2019 a 2023 a Enugu.

4. Ribas

Gwamna Nyesom Wike ya sha alwashin yakar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa. Akwai yiwuwar hakan ya taimaki LP a zaben 2023.

Atiku Abubakar da Peter Obi
Atiku Abubakar da Peter Obi a zaben 2019 Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

5. Kuros Ribas

Jam’iyyar PDP ba ta da gwamna a Kuros Riba, kuma APC ba ta da karfi sosai. Akwai jiga-jigan siyasar jihar da za su taimakawa takarar Peter Obi.

6. Taraba

Duk da karfin PDP, babu mamaki wasu yankunan jihar Taraba su zabi Peter Obi a badi, musamman yadda jam’iyyar LP ta ba John Ikenya takarar gwamna.

7. Benuwai

Alamu na kara nuna cewa Gwamna Samuel Ortom da manyan jihar Benuwai ba za su goyi bayan PDP a zaben shugaban kasa ba, watakila su zabi LP.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Jiga-Jigan 'Yan PDP Da Suka Yi Watsi Da Atiku Suka Rungumi Obi

8. Filato

Ba abin mamaki ba ne tsohon gwamnan Anambra ya ba PDP har da APC mamaki a Filato. Ba wannan ne karon farko da LP ta ci zabe a jihar ba.

Dalilin komawar Rabiu Kwankwaso NNPP

Kun ji labari Dr. Rabiu Kwankwaso ya nemi Mohammed Jamu ya samu mukami a PDP, amma wasu jiga-jigan jam’iyya suka hana a ba shi kujerar.

A dalilin wannan ne Jamu yace aka fusata Rabiu Musa Kwankwaso har ta kai ya koma jam’iyyar NNPP yana takarar shugabancin kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel