2023: Sabuwar Na’urar BVAS da INEC ta Kawo Za ta Hana Magudin Zabe

2023: Sabuwar Na’urar BVAS da INEC ta Kawo Za ta Hana Magudin Zabe

  • Victor Ndoma-Egba ya yaba da cigaban da hukumar INEC ta zo da shi domin gyara harkar zabe a Najeriya
  • Sanata Victor Ndoma-Egba yace BVAS da sauran fasahohin da aka zo da su za su taimakawa APC ne
  • Tsohon ‘dan majalisa ya bayyana haka yayin da ya karbi bakuncin ‘yan APC National Integrity Movement

Abuja - Sanata Victor Ndoma-Egba ya nuna yana goyon bayan amfani da na’urorin BVAS da hukumar INEC za tayi a zaben shekara mai zuwa.

Daily Trust ta rahoto tsohon jagora a majalisar dattawan yana cewa BVAS da sauran fasahohin zamani a za ayi amfani da su za su inganta zabe.

Victor Ndoma-Egba ya yi wannan jawabi a garin Abuja a lokacin da ‘ya ‘yan kungiyar 'APC National Integrity Movement' suka kai masa ziyara.

Kara karanta wannan

"Dalilin Da Yasa Cikin Sauki Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasan 2023"

Da aka kai masa ziyara har gidansa a Abuja, ‘dan siyasar ya shaidawa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC cewa cigaban da aka kawo zai canza harkar zabe.

BVAS zai taimakawa APC - Ndoma-Egba

A cewar Victor Ndoma-Egba, fasahohin da za ayi amfani da su za su taimakawa jam’iyyarsu ta APC mai mulki wajen samun galaba a zaben badi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jagoran na APC yace zaben 2023 zai sha ban-bam da na baya domin wadannan cigaba na fasaha da kara wayewa da masu kada kuri’a suka yi.

Na'urar BVAS
Na'urar BVAS a wajen zabe Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

A jawabinsa, Sanata Victor Ndoma-Egba yace tafiyar EndSARS ta kara buda masu idanu a kan yadda za ayi amfani da jama’a a wajen kawo sauyi.

Tsohon ‘dan majalisar ya yaba da tafiyar wannan kungiya, yace ko bayan gama zabe, ya kamata a dage da taimakawa jam’iyya ba saboda dukiya ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani Na APC a Wata Jiha, Ta Yi Fatali da Wadanda Suka Ci Zabe

Ndoma-Egba ya wakilci Kuros Ribas ta tsakiya na tsawon shekaru 12 a majalisar dattawa.

...a karshe mu za mu ci zabe - Abubakar Sa’adu

Da yake na sa jawabin, shugaban wannan tafiya na kasa, Abubakar Sa’adu yace kungiyarsu za tayi kokarin wajen ganin fasahohin sun taimake su.

Abubakar Sa'adu yake cewa jam’iyya mai mulki za ta amfana domin suna da mabiya a duk lungunan kasar nan, kuma suna da ayyukan da za su tallata.

Komai ya wuce - Tinubu

An samu labari magoya baya sun shiga sun fita, sun roki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Farfesa Yemi Osinbajo afuwa, a tafi tare a jam'iyya.

‘Dan takaran shugaban kasar ya shaidawa jama’a ya hakura da abin da ya faru a zaben gwani, kuma zai yi aiki da kowam har da tsohon yaron na sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng