Bana Tsoron Gwamna Mai Ci, Inji Dan Takarar Gwamnan NNPP a Jihar Gombe
- Dan takarar gwamnan NNPP a jihar Gombe ya bayyana kadan daga karfin gwiwar da yake dashi a zaben 2023 mai zuwa
- Khamisu Mailantarki ya ce baya tsoron gwamna mai ci a Gombe, don haka tumbuke shi abu ne mai sauki a wurinsa
- Dan takarar ya taba yiwa kujerar majalisar wakilai ta tarayya zuwa daya a sabuwar jam'iyyar CPC a zaben 2011
JIhar Gombe - Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar NNPP mai kayan marmari a jihar Gombe, Khamisu Mailantarki ya ce sam karfin ikon gwamna Inuwa bai bashi ciwon kai, zai iya lallasa shi a zaben 2023.
Mailantarki ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da wakilin jaridar Leadership, inda yace shi ya saba da tumbuke shugabannin dake kan karagar mulki.
Mai lantarki ya bayyana cewa, kasancewarsa a jam'iyyar NNPP ba yana nufin yana da rauni bane, zai yi iya kokarinsa da ya saba yi wurin samun nasara kan jam'iyyu sanannu a kasar nan.
Na karbi kujerar majalisa duk da kuwa daga sabuwar jam'iyya na fito, inji Mailantarki
Da yake tuna sa'arsa, ya ce ya zama dan majalisar tarayya na mazabar Gombe/Kwami a majalisar tarayya a 2011 duk da kuwa ya fito ne a sabuwar jam'iyya ta CPC.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma bayyana cewa, ya samu nasarar yin haka ne duk da kuwa cewa wanda yake kan kujerar a wancan lokacin sananne ne kuma a karkashin sananniyar jam'iyya.
A kalamansa:
"Wannan kyakkyawar tunatarwa ce ga ma dukkan mutanen jihar Gombe. A 2011 lokacin da na yi takara, a lokacin ne na fara tafiyar siyasa.
"Na duba jihar, na kuma duba abin dake faruwa sannan na ga tagar cewa, mutanen Gombe masana ne a fannin siyasa da sauransu.
"To, maganar zama kan karaga, siyasar uban gida bata aiki a jihar Gombe. Kawai fadi ake da kuma tunanin haka. Na tabbatar da hakan a 2011, lokacin da naga taga, lokacin da muka yi imanin za mu yi abu mai kyau fiye da me ake yi."
Wancan lokacin ma albarkacin kaunar Buhari ya ci, in Muhammad Jibrin
Bayan wani dan lokaci, Legit.ng Hausa ta tattauna da wani malamin jami'a kuma mai sharhi kan siyasar jihar Gombe, Muhammadu Jibrin, wanda ya yi waiwaye zuwa ga tafiyar siyasar Mailantarki.
Ya tuna cewa, a lokacin da Mailantarki ya lashe zaben 2011, a lokacin 'yan Najeriya na matukar kaunar ganin Buhari ya ci zabe, don haka kasancewarsu a jam'iyyar daya ta taimake shi.
A cewarsa:
"Idan ka duba shi Mailantarki, ai ya ci zabe ne a 2011 albarkacin Buhari. To yanzu Kwankwaso na da karbuwa irinta Buhari ne? Kwankwasi ne dai aka fi sani a NNPP, kuma bai da karbuwar Buhari.
"Sannan idan ka duba, ai Mailantarki farin jininsa ya shude, a matsayinka na dan jarida da za ka fita ka tambayi mutane biyar zuwa zuwa goma alherinsa, za ka ji basu san me za su ce ba, to ina zai tafi.
"A bangaren tasiri, bana goyon bayan gwamnan yanzu, saboda bana kebe tsagi a siyasa, amma nasan Inuwa ya yi aikin da ya dace, kuma ya ci alkawuransa, don haka mutanen Gombe za su fi yarda da Inuwa fiye da Mailantarki."
Idan Cin Bashi Laifi Ne, Da Yanzu Amurka Ta Zama Magarkama, Inji Tinubu
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya yi watsi da damuwar da 'yan Najeriya ke ciki na bashin da ake bin kasar.
Tinubu ya bayyana cewa, da ace cin bashi laifi ne, da yanzu haka ilahirin kasar Amurka ta zama magarkama saboda tudun bashi, rahoton TheCable.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a 21 ga watan Oktoba yayin ayyana manufofinsa gabanin babban zaben 2023.
Asali: Legit.ng