2023: Dan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa PDP a Oyo

2023: Dan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa PDP a Oyo

  • Ɗan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar ADC a jihar Oyo, Emmanuel Oyewole, ya koma PDP
  • Mista Oyewole yace gwamnatin Makinde ta yi abin a zo a gani a zangon farko, don haka ta cancanci zarcewa kan madafun iko
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da jam'iyyar PDP ke fama da rikicin cikin gida tsakanin gwamna Wike da Atiku

Oyo - Emmanuel Oyewole, abokin takarar mai neman zama gwamnan jihar Oyo karkashin inuwar jam'iyyar ADC a 2023, ya koma jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa Mista Oyewole ya sanar da matakin sauya shekarsa zuwa jam'iyyar PDP ne ranar Jumu'a a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Emmanuel Oyewole.
2023: Dan Takarar Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa PDP a Oyo Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa Dakta Ganiyu Ajadi, shi ne ɗan takarar gwamnan Oyo a inuwar jam'iyyar African Democratic Congress, watau ADC a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Gangamin Taron Kamfen PDP a Edo Ya Sake Fito da Rikicin Jam'iyyar, Atiku Ya Shiga Matsala

Da yake jawabi a ɗakin taron kungiyar yan jarida (NUJ), Oyewole yace ya koma PDP domin ba da gudummuwa ga tazarcen mai girma gwamna Seyi Makinde.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ni da mabiya na dake lungu da sakon jihar nan mun yi nazari kan ɗaukar wannan matakin kuma zan iya cewa na yanke komawa PDP ne saboda ƙaunar jihar Oyo."
"Gaskiya a bayyane take, idan muka duba jagoranci mai kyau da gogewar gwamnatin Makinde to kamata ya yi ace ɗan takara ɗaya ne tal a jihar nan a zaben 2023."
"Kuma wannan ɗan takara ba kowa bane face gwamnan da ke kan madafun iko yanzu haka saboda suna cewa zango ɗaya mai kyau ya cancani a sake ba shi dama ta biyu."

- Emmanuel Oyewole.

Makinde ya maida mafarkin mutane zuwa gaskiya - Oyewole

Kara karanta wannan

Na Kusa da Gwamnan Arewa, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Mista Oywole ya kara da cewa gwamnatin Seyi Makinde na ci gaba da cika mafarkan mazauna jihar Oyo a hankali a hankali.

A cewarsa nasarorin da gwamnatin Oyo ta samu a bangaren manyan ayyukan ci gaba, faɗaɗa tattalin arziki da walwalar al'umma ta zarce matasayin yabo kaɗai.

Bugu da ƙari, yace Makinde ya yi abin a zo a gani a ɓangarorin da suka haɗa za Ilimi, tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Fitar da Sunayen Tawagar Kamfen 2023 Na Karshe, An Samu Sauyi

Jam'iyyar APC mai mulki fa fitar da sunayen mambobin tawagar yakin neman zaɓen 2023 na karshe.

Manyan kusoshin jam'iyyar da suka haɗa da gwamnoni sun nuna rashin amince wa da tawagar farko, lamarin da ya jawo tsaiko a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel