Gwamnan APC Ya Zakulo Mata 16, Ya Raba Masu Muhimman Mukamai a Gwamnatinsa

Gwamnan APC Ya Zakulo Mata 16, Ya Raba Masu Muhimman Mukamai a Gwamnatinsa

  • A makon nan aka ji Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya sake raba wasu mukamai a gwamnati ga mata
  • Gwamnan na Jihar Kwara ya kama hanyar yin abin da babu wata jiha da tayi, ya warewa mata mukamai birjik
  • Mai girma AbdulRahman AbdulRazaq ya dauko mace daga kowace karamar hukuma, ya ba ta kujerar SA

Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya zabi mata 16, ya nada su a matsayin masu taimaka masa wajen cin ma manufofin SDG.

Rahoton da Daily Trust ta fitar a yammacin Alhamis, 20 ga watan Oktoba 2022, yace Mai girma Gwamnan ya dauko mace daya daga kowace karamar hukuma.

Matan za suyi aiki a matsayin masu taimakawa na musamman a ofishin gwamnan Kwara.

Wadannan mata da suka zama Hadiman Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, za su bada gudumuwarsu ne domin ganin gwamnatinsa ta cin ma nasara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Wata Jiha a Najeriya Ya Rasu

Matan da suka samu mukamin SAs

Wadanda aka ba mukaman sun hada da: Usman Bilikis, Monsurat Lawal, Khadijat Ibrahim, Jibola Yusuf, Abdulmumin Habibat, da Dorcas Toyin Ogunwole.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau akwai Aishat Motunrayo Yusuf, Deborah Lawal, Kafayat Kazeem da Titilayo Ashaolu.

Legit.ng tace ragowar su ne Oluwakemi O. Afolashade, Sani Kudirat, Esther Funlola Adejumo, Amudat Muhammad, Fatima Mohammed, da Kashi Mohammed.

Gwamnan Kwara
Gwamnan Kwara yana ganawa da mutanensa Hoto: @RealAARahman
Asali: Twitter

Ana yi da mata a Gwamnatin Kwara

A baya gwamna AbdulRazaq ya sa hannu a dokar da ta wajabtawa gwamnatin jihar nada mata su zama akalla 35% a majalisar zartarwa da sauran mukamai.

Dole idan za a raba kujerun gwamnati, sai an dama da mata a jihar Kwara. Yanzu haka akwai kwamishinoni 12 da duk mata ne a gwamnatin AbdulRazaq.

Baya ga kwamishinoni, rahoton yace daga cikin manyan sakatarorin din-din-din da Gwamnan ya nada a ma’aikatun gwamnatin Kwara, a yau akwai mata 12.

Kara karanta wannan

Kwankwaso @66: Wasu abubuwa 10 da ba ka sani ba a game da ‘Dan Takaran NNPP

Bugu da kari mata suna rike da manyan cibiyoyin gwamnati a jihar Kwara irinsu hukumar nan ta Kwara Revenue Service (KWIRS) mai alhakin tara haraji.

Dangote v Gwamnatin Kogi

Kun ji labari Gwamnatin Kogi ta je kotu, tana so a hana kamfanin Dangote amfani da kamfanin simintin Obajana da ke karamar hukumar Oworo a jihar Kogi.

Lauyoyin Gwamnatin Yahaya Bello sun bukaci kotu ta duba tsofaffin yarjejeniyar da Jihar Kogi ta shiga da Aliko Dangote a 2002, tana zargin an rasa ginshiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel