Wani Fasto Ya Fadawa PDP Abin da Za Ayi Domin a Ceci Jam’iyyar Adawa a 2023
- Fasto Godfrey Gbuji yana goyon bayan Nyesom Wike da yace wajibi ne Iyorchia Ayu ya yi murabus
- Limamin na cocin Royal House of David a Imo yana ganin canza Ayu ne zai ba Jam'iyyar PDP nasara
- Faston ya yi kira cewa a samu sabon shugaban PDP na kasa daga yankin Kudu maso gabashin Najeriya
Imo - Godfrey Gbuji wanda shahararren Fasto ne a cocin 'Royal House of David', yace Sanata Iyorchia Ayu ne kadai zai iya ceton jam’iyyar PDP.
Vanguard ta rahoto Fasto Godfrey Gbujie yana cewa idan PDP tana neman kwanciyar hankali, dole Iyorchia Ayu ya yi murabus daga kan kujerarsa.
Faston ya yi wannan bayani lokacin da ya zanta da manema labarai a garin Owerri, jihar Imo.
Gbujie yake cewa jam’iyyar da aka kafa a kan adalci da gaskiya, bai dace ta saki layi ba, yana ganin bai kamata Ayu ya cigaba da jagorantar NWC ba.
A dalilin wannan, Faston yace yana goyon bayan kiran da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike yake yi na cewa shugaban na jam’iyyar PDP ya sauka.
Malamin addinin wanda ya shiga harkar siyasa tsudum yace abin da ya dace ayi shi ne shugaban jam’iyyar PDP ya fito daga kudu maso gabas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Godfrey Gbujie yace idan Dr. Iyorchia Ayu ya dage cewa ba zai bar ofis ba, jam’iyyarsa ta PDP za ta ga mummunan sakamakon a zaben shekara mai zuwa.
Malamin addinin ya koka a kan yadda Ayu ya shirya zaben fitar da gwanin shugaban kasa wanda ya ba Alhaji Atiku Abubakar nasara a kan Gwamna Wike.
Baya ga haka, Gbujie ya nunawa manema labarai cewa bai dace shugaban PDP na kasa ya rike kujerarsa ba la’akari da sabanin addini da na bangaranci.
Zaben shugaban kasa a 2023
Jaridar nan ta Leadership ta rahoto Faston yana cewa ya shiga siyasa ne ta karkashin tafiyar su ta 'Divine International Christian Movement'.
Har ila yau, an ji wannan babban fasto da yake jagorantar Kiristoci a jihar Imo yace babu wanda ya isa ya kawo cikas ga zaben 2023, kuma ya zauna lafiya.
Takarar Peter Obi a LP
Dazu An ji labari jigon APC, Aminu Dabo ya nesanta kan shi da takarar Peter Obi, yace LP ta sa sunansa a kwamitin kamfe ba tare da an tuntube shi ba.
Arch. Aminu Dabo ya fadawa Peter Obi cewa kyau ya hakura da neman kujerar shugaban kasar Najeriya a 2023, ya marawa Bola Tinubu baya a APC.
Asali: Legit.ng