Yanzu Yanzu: Wike Yace Ba Atiku Kadai Bane Dan Takarar PDP

Yanzu Yanzu: Wike Yace Ba Atiku Kadai Bane Dan Takarar PDP

  • Gwamna Nyesom Wike ya bayyana gaskiyar lamari game da rikicinsa da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar
  • Wike ya bayyana cewa shugabancin jam’iyyar na sane da matsayinsa da kuma dalilinsa na ci gaba da tada jijiyoyin wuya
  • Yayin da rikici ke kara kamari, watanni kafin zaben 2023, Wike yace ya mayar da hankali wajen yiwa jam’iyyar adawar kamfen a jiharsa

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya jadadda cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ba shi kadai ne dan takarar jam’iyyar ba.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 14 ga watan Oktoba yayin da yake zantawa da manema labarai.

Nyesom Wike
Yanzu Yanzu: Wike Yace Ba Atiku Kadai Bane Dan Takarar PDP Hoto: Atiku Abubakar, Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Jigon na PDP ya bayyana hakan ne yayin da yace ya mayar da hankali wajen yiwa jam’iyyar adawar kamfen a jihar Ribas, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike Ya Dauki Ortom, Makinde Da Ikpeazu Sun Shilla Kasar Waje, An Bayyana Dalilin Fitarsu

Rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawar kasar na kara muni yayin da gwamnan na jihar Ribas da wasu fusatattun ‘ya’yan jamiyyyar suka nace lallai sai Ayu ya yi murabus,

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika suna so a karbe kujerar shugabancin jam’iyyar na kasa daga arewa zuwa yankin kudancin Najeriya.

Rikici Ya Kara Tsanani, Gwamna Wike Ya Sha Alwashin Ba Zai Bar Arewa Ta Mamaye Komai a PDP Ba

A gefe guda, mun ji cewa yayin da rikici ke kara kamari a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sha alwashin cewa, ba zai bari 'yan Arewa su ci gaba da mamaye manyan kujeru a jam'iyyar ba.

Wike ya yi watsi da tsarin da jam’iyyar ke kai a yanzu haka inda manyan masu rike da mukamai suka fito daga yankin arewacin kasar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ayu Yayi Martani Kan Zarginsa da Wike Yayi na Cin Rashawar N100m da N1b

Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu; dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Aminu Tambuwal duk 'yan arewa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel