Rikici ya Bijirowa PDP, An Dakatar da Na Hannun Daman El-Rufai da Wasu Shugabanni

Rikici ya Bijirowa PDP, An Dakatar da Na Hannun Daman El-Rufai da Wasu Shugabanni

  • Babu zaman lafiya a PDP duk da kotu ta bukaci a sake zaben fitar da gwani na zaben Gwamnan Ogun
  • Jimi Lawal da mutanensa sun shirya zaben tsaida ‘dan takara, wanda hakan ya jawo masu fushin jam’iyya
  • Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ogun ta bada sanarwar dakatar da ‘ya ‘yan na ta ne a kan sabawa doka

Ogun - Rikici ya barke a jam’iyyar PDP na reshen jihar Ogun a farkon makon nan, inda aka zargi Jimi Lawal da shirya zaben tsaida gwani na bogi.

Daily Trust tace ana tuhumar Jimi Lawal da laifin gudanarwa da kuma shiga zaben fitar da gwanin gwamna a jam’iyyar PDP wanda ya sabawa doka.

Baya ga Lawal, an dakatar da Bola Odunmosun wanda shi ne sakataren kudi na jam’iyyar da kuma Fasiu Ajadi, Kola Akinyemi sai wani Tope Asiru.

Kara karanta wannan

Sunan Darektan Kamfe a APC Ya Fito a Kwamitin Yakin Neman Zaben Peter Obi

Tope Asiru shi ne shugaban PDP na karamar hukumar Ijebu ta Arewa maso gabas a jihar Ogun.

Jam'iyya ta bada sanarwar dakatar da su Lawal

Daily Post tace sakataren yada labaran PDP na reshen Ogun, Sunday Solarin ne ya bada sanarwar dakatar da wadannan jagororin daga jam’iyyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Sunday Solarin, wadanda aka dakatar sun saba tsarin mulkin jam’iyya ta hanyar shiga cikin zaben fitar da gwani ba tare da bin ka’ida ba.

Na Hannun Daman El-Rufai
Jimi Lawal da Nasir El-Rufai Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Hujjar da jam’iyyar ta bada shi ne majalisar aiwatarwa na NWC ba ta san da zaman wannan zaben tsaida ‘dan takara da su Jimi Lawal suka shirya ba.

Ba za ta sabu ba - Jimi Lawal

A wani raddi da ya yi, Vanguard ta rahoto Lawal yana mai cewa dakatarwar da PDP take ikirarin tayi masa daga jam’iyya sam ba zai iya yin aiki ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: APC ta Aikewa INEC Wasika, Ta Bukaci a Karba Machina ‘Dan Takarar Sanata

Darektan kwamitin yakin neman zaben Jimi Adebisi Lawal watau Austin Oniyokor ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a garin Abeokuta.

Austin Oniyokor yake cewa abin da shugabannin PDP na jihar suka yi, ya ci karo da hukuncin kotu wanda yace a sake shirya wani zaben ‘dan takara.

Kamar yadda Oniyokor ya fada, wadanda suka dauki wannan mataki suna aiki ne a karkashin umarnin daya daga cikin wadanda ya sha kashi a zaben.

Sabani a jam'iyyar APC

A baya an ji labari tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun yace ba zai marawa jam’iyyar APC baya a zaben Gwamna jiha da za ayi a farkon 2023 ba.

Sanata Ibikunle Amosun yace zai goyi bayan jam’iyyar African Democratic Congress ta doke APC. Biyi Otegbeye ne mai neman zama gwamna a inuwar ADC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel