Da Duminsa: APC ta Aikewa INEC Wasika, Ta Bukaci a Karba Machina ‘Dan Takarar Sanata

Da Duminsa: APC ta Aikewa INEC Wasika, Ta Bukaci a Karba Machina ‘Dan Takarar Sanata

  • Hedkwatar jam’iyyar APC ta kasa ta aikewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC wasika kan ta amince tare da wallafa sunan Machina matsayin ‘dan takarar sanata
  • Wasikar ta samu saka hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da sakataren jam’iyyar na kasa kuma sun mika ta ga INEC
  • Hakan ya kasance biyayya ga umarnin kotun tarayya mai zama Damaturu wacce tace Machina ne halastaccen ‘dan takarar Sanata na Yobe ta arewa

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta aikewa Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC wasika inda ta umarci Hukumar zaben da ta karba Bashir Sheriff Machina a matsayin ‘dan takarar kujerar sanata na mazabar Yobe ta arewa.

Channels TV ta rahoto cewa, wannan matakin da APC ta dauka biyayya cewa umarnin babbar kotun tarayya dake Damaturu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

Machina da Lawan
Da Duminsa: APC ta Aikewa INEC Wasika, Ta Bukaci a Karba Machina ‘Dan Takarar Sanata. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Kotun wacce ta samu jagorancin Alkali Fadima Aminu ta umarci INEC da ta karba tare da wallafa sunan Machina matsayin ‘dan takarar yankin inda ta jaddada ingancin zaben fidda gwani da aka yi a ranar 28 ga watan Mayu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sa’o’i kadan bayan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya amince da hukuncin kotun, shugabancin jam’iyyar ya bayyana cewa zai daukaka kara.

Amma a wasikar shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu da sakataren jam’iyyar, Sanata Iyiola Omisore suka saka hannu, APC ta umarci INEC da ta wallafa sunan Machina a shafinta na yanar gizo domin biyayya ga umarnin kotun.

“Mun rubuto ne domin sanar da hukumar kan hukuncin kotu ai kwanan wata 28 ga watan Satumban 2022 da umarnin ranar 5 ga watan Oktoban 2022 daga babbar kotun tarayya mai zama a Damaturu wacce ta bukaci hukumar da ta karba Bashir Sheriff matsayin ‘dan takarar sanata na Yobe ta arewa kuma ta wallafa sunansa.”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU ta Janye Yajin Aiki

- Wasikar mai kwanan wata 10 ga Oktoban 2022 tace.

Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan

A wani labari na daban, duka biyu kenan ga shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan. 'Dan takarar kujerar sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a karkashin jam'iyyar APC kuma wanda ya ci zaben fidda gwani, Bashir Machina, ya ki janyewa Lawan.

Lawan, wanda ke wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa, ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu a zaben fidda gwani na neman tikitin takarar shugabancin kasa da aka yi a ranar 8 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel