Rikicin PDP: Dalilin da Yasa Na Yi Murabus Daga Shugaban BoT Na Kasa, Jibrin Ya Fadi Gaskiya

Rikicin PDP: Dalilin da Yasa Na Yi Murabus Daga Shugaban BoT Na Kasa, Jibrin Ya Fadi Gaskiya

  • Tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar pdp, Walid Jibrin, ya bayyana ainahin dalilinsa na yin murabus
  • Jibrin ya ce ya sauka daga mukaminsa ne domin ganin an zauna lafiya a babbar jam'iyyar adawar kasar
  • Tsohon sanatan ya jadadda cewa ba za a taba samun ci gaba a Najeriya ba idan har ba a guje ma siyasar kabilanci, bangarenci da addini ba

Nasarawa - Nigerian Tribune ta rahoto cewa tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Walid Jibrin, ya magantu a kan murabus da yayi daga kujerarsa.

A farkon watan Satumba ne Jibrin wanda ya kasance tsohon sanata, ya sanar da murabus dinsa a taron BoT na PDP da ya gudana a Abuja.

Ya sauka daga kujerarsa ne a daidai lokacin da aka matsa lamba wajen kira ga sauya fasalin shugabancin jam’iyyar wanda ya baiwa yankin arewacin kasar fifiko.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Kara Tsanani, Gwamna Wike Ya Sha Alwashin Ba Zai Bar Arewa Ta Mamaye Komai a PDP Ba

Walid Jibrin
Rikicin PDP: Dalilin da Yasa Na Yi Murabus Daga Shugaban BoT Na Kasa, Jibrin Ya Fadi Gaskiya Hoto: Nigerian Tribune

Daga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar har zuwa shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu duk yan arewa ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jiga-jigan jam’iyyar musamman daga yankin kudancin kasar sun ce lallai sai Ayu yayi murabus daga kujerarsa domin yin adalci.

Sai dai kuma, maimakon Ayu, Jibrin ya baiwa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar mamaki bayan ya sanar da murabus dinsa.

Ficewarsa bai sanyaya wutar rikicin da ke ta kara huruwa a jam’iyyar ba domin jiga-jigan kudu sun ce lallai sai Ayu yayi murabus sannan abubuwa zasu lafa.

Jibrin ya sanar da magoya bayan jam’iyyar a yayin kaddamar da kwamitin kamfen dinta a jihar Nasarawa cewa ya yi murabus ne domin samar da zaman lafiya da aminci a jam’iyyar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Ya ce:

“Na yi murabus daga matsayin shugaban BoT ne don samar da zaman lafiya a jam’iyyar da kuma ba sauran jiga-jigan jam’iyyar da basu taba hawa tsohon matsayina ba damar yin haka.”

Kara karanta wannan

Sanatan Kano Ya Bayyana Ainahin Wanda Osinbajo Yake Goyon Baya A Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Ya yi watsi da abun da ya kira da siyasar kabilanci, bangaranci da addini, yana mai cewa kasar ba za ta taba samun ci gaba ba idan har ba a kauracewa irin wadannan abubuwan ba.

Ya ce babbar jam’iyyar adawar kasar za ta magance rikicin da ke tsakanin tsagin dan takararta na shugaban kasa da tsagin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kwanan nan, gabannin fara kamfen din 2023.

Ya nuna tabbacin cewa PDP za ta lashe zaben shugaban kasa da jihohi da dama a zabe mai zuwa yayin da ya bukaci mambobin jam’iyyar da su dinke baraka.

Rikici Ya Kara Tsanani, Gwamna Wike Ya Sha Alwashin Ba Zai Bar Arewa Ta Mamaye Komai a PDP Ba

A gefe guda, mun ji cewa yayin da rikici ke kara kamari a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sha alwashin cewa, ba zai bari 'yan Arewa su ci gaba da mamaye manyan kujeru a jam'iyyar ba.

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

Wike ya yi watsi da tsarin da jam’iyyar ke kai a yanzu haka inda manyan masu rike da mukamai suka fito daga yankin arewacin kasar.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu; dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Aminu Tambuwal duk 'yan arewa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel