Kwankwaso Ya Kaddamar Da Ofishin NNPP A Lagos, Ya Ce Jam'iyyar 'Ta Yi Karfi Tamkar APC Da PDP'

Kwankwaso Ya Kaddamar Da Ofishin NNPP A Lagos, Ya Ce Jam'iyyar 'Ta Yi Karfi Tamkar APC Da PDP'

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya kadamar da ofishin jam'iyyar a Legas
  • Daruruwan mutane sun halarci bikin bude ofishin da aka yi a Ikorodu Road, wadda hakan ya janyo cinkoson ababen hawa a yankin
  • Kwankwaso, a jawabinsa wurin taron ya ce jam'iyyar ta NNPP yanzu ta bunkasa ta kai matsayin da za ta iya fafatawa da APC da PDP a zaben 2023

Jihar Legas - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, a ranar Laraba, ya kaddamar da ofishin jam'iyyar a Jihar Legas.

A wurin bikin kadamarwar ofishin da ke Ikorodu Road, Kwankwaso ya fada wa magoya bayan jam'iyyar, har da wadanda suka shigo daga wasu jam'iyyun cewa jam'iyyar ta kara karfi tun bayan shigowarsa kuma za ta iya fafatawa da manyan jam'iyyun kasar biyu - APC mai mulki da babban jam'iyyar hamayya, PDP.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Riga Ta Fatattaki Kanta Daga Mulki, In Ji Dan Takarar PDP A Kwara, Yaman

Kwankwaso A Legas
Kwankwaso Ya Kaddamar Da Ofishin NNPP A Lagos, Ya Ce Jam'iyyar 'Ta Yi Karfi Tamkar APC Da PDP'. Hoto: Saifullahi Hassan.
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya koma jam'iyyar ta NNPP ne a watan Maris daga PDP bayan ya rasa karfin iko a jam'iyyar a jihar Kano, Premium Times ta rahoto.

Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan, a wurin taron a Legas, ya ce tsohon gwamnan na jihar Kano ta yi alkawarin bawa ilimi da cigaban matasa muhimmanci idan an zabe shi shugaban kasa a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

NNPP Legas
Ofishin NNPP A Legas. Hoto: Saifullahi Hassan.
Asali: Facebook

NNPP Legas
Magoya baya da mambobin NNPP A Legas. Hoto: Saifullahi Hassan.
Asali: Facebook

Kwankwaso, wanda shugabannin jam'iyyar na kudu maso yamma da dandazon magoya baya suka yi wa rakiya ya kara da cewa NNPP a yanzu tana aji daya ne da manyan jam'iyyun kasar duk da bata dade da yin fice ba.

Kwankwaso ya bayyana yawan magoya baya a matsayin allama da ke nuna cewa mutane sun amince da sakonsa na takarar shugaban kasa kuma zai yi nasara a 2023.

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

Da ya ke alfahari da ayyukan da ya yi a baya, Kwankwaso ya yi alkawarin tafiya tare da matasa ta hanyar bada ilimi a dukkan matakai, yayin da ya jadada nufinsa na karfafa wa matasa gwiwa ta kawo karshen rashin tsaro da ke adabar kasar.

2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu

A wani rahoton, mutum hudu cikin wadanda za su yi takara a zaben 2023 karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a Jihar Osun, a ranar Laraba sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Bola Tinubu.

Yan takarar, Clement Bamigbola, dan takarar sanata na Osun Central; Bolaji Akinyode, dan takarar sanata na Osun West; Olalekan Fabayo da Oluwaseyi Ajayi, yan takarar majalisar tarayya na Boluwaduro/Ifedayo/Ila, da Ijesa South kamar yadda aka jero.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164