2023: APC Ta Riga Ta Fatattaki Kanta Daga Mulki, In Ji Dan Takarar PDP A Kwara, Yaman

2023: APC Ta Riga Ta Fatattaki Kanta Daga Mulki, In Ji Dan Takarar PDP A Kwara, Yaman

  • Alhaji Abdullahi Shuaib Yaman, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Jihar Kwara ya ragargaji jam'iyyar APC
  • Yaman ya ce jam'iyyar ta APC ta riga ta fatattaki kanta daga mulki soboda rashin tabuka wani abin a-zo-a-gani a jihar tsawon shekaru 3 da suka shude
  • Tsohon kwamishinan na RMAFC ya ce gwamnatin APC ta jefa Kwara cikin bashi kuma ta gaza habbaka albarkatun da ke jihar

Kwara - Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Alhaji Abdullahi Shuaib Yaman, ya ce idan aka yi la'akari da abin da ta yi tsawon shekaru 3 a Kwara, jam'iyyar APC ta kori kanta daga mulki.

Yaman ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa da aka yi da mambobin kungiyar yan jarida na Najeriya, NUJ, reshen jihar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu, gwamnonin APC da jiga-jigai sun shiga wata ganawa mai muhimmanci

Alhaji Yaman
APC Ta Riga Ta Fatattki Kanta Daga Mulki, Dan Takarar PDP A Kwara, Yaman. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

A cewarsa, jam'iyyar mai mulki ta mayar da jihar Kwara baya kuma ta yi gaza yin tunanin hanyoyin da za ta samar da arziki a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan takarar na PDP, tsohon kwamishina a Hukumar tattara kudaden shiga da kasafin kudi, RAMFC, ya ce APC ta jefa jihar cikin bashi.

Ya ce idan aka zabe shi a 2023, gwamnatin PDP za ta yi amfani da albarkatun da jihar ke da shi don bunkasa tattalin arziki.

APC ba ta tabuka komai ba a mulkin shekaru uku da ta yi a Kwara, Yaman

Wani sashi na kalamansa:

"APC ta riga ta fatattaki kanta daga mulki saboda rashin iya jagoranci. Masu zabe ba su yin tambayoyi masu muhimmanci. Gwamnati ta gari ba za ta jefa jiha cikin bashi ba.
"Jihar Kwara na da isassun albarkatu da za ta iya kirkiran ayyuka ga matasan inda za mu samu haraji da za a saka ayyuka kamar ilimi, lafiya, da walwala da jin dadin mutane.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Yan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Da Suka Yi Rajista Da Satifiket Din WAEC/SSCE Kacal

"Ba kawai a tafi Abuja duk wata a karbo kudi daga riban man fetur ba a kawo Kwara a kashe. Kowane mutum zai iya kashe kudi don haka ba abin da aka zabi gwamna ya yi ba kenan."

Ya kara da cewa:

"A halin yanzu da muke magana, bashin da ake bin Jihar Kwara ya ci Naira biliyan 100 kuma muna biyan N1.3 biliyan duk wata a kan bashin."

Ya zargi gwamnatin APC da rashin iya aiki, yana mai cewa ba ta iganta Jihar Kwara ba kamar yadda ta yi alkawari a 2019.

2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu

A wani rahoton, mutum hudu cikin wadanda za su yi takara a zaben 2023 karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a Jihar Osun, a ranar Laraba sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

Yan takarar, Clement Bamigbola, dan takarar sanata na Osun Central; Bolaji Akinyode, dan takarar sanata na Osun West; Olalekan Fabayo da Oluwaseyi Ajayi, yan takarar majalisar tarayya na Boluwaduro/Ifedayo/Ila, da Ijesa South kamar yadda aka jero.

Asali: Legit.ng

Online view pixel