Jiga-jigan APC, Tinubu da Gwamnonin Jam'iyyar Sun Shiga Wata Muhimmiyar Ganawa a Abuja
- Yanzu muke samun labarin cewa, kwamitocin jam'iyyar APC sun shiga ganawa don warware wasu matsalolin jam'iyyar
- Dan takarar shugaban kasan APC, Bola Ahmad Tinubu da gwamnonin jam'iyyar duk sun hallara domin wannan zama
- Hakazalika, akwai jiga-jigai da dama dake cikin kwamitin gangamin kamfen din APC na dan takarar shugaban kasa
Abuja - Ganawar tawaga uku ta jam'iyyar APC da ta hada kwamitin ayyukanta na kasa (NWC) da tawagar gangamin kamfen na 'yan takarar gwamnoni da shugaban kasa sun taru domin tattawa mai zurfi.
Ana yin wannan ganawar ne a Hilton Hotel dake babban birnin tarayya Abuja, The Nation ta ruwaito.
Ganawar, wacce aka ce ci gaban zaman tagawar ne na baya, zata kawo mafita ne da warware duk wata kimurmura a jerin mambobin majalisun kamfen na jam'iyyar a fadin kasar.
Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2
Hakazalika, zaman zai duba yiwuwar tabbatarwa tare da amincewa da jerin shugabannin PCC da gwamna Simon Lalong ya shirya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wadanda suka halarci taron sun hada da dan takarar shugaban kasan jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, gwamnoni da mambobin PCC na APC.
A baya an shirya yin taron ne a jiya Talata 11 ga watan Oktoba, amma aka daga saboda bikin ba da lambobin yabon kasa da gwamnatin Buhari ta yi a ranar.
Hakazalika, Sanata Kashim Shettima na daga cikin wadanda suka halarci taron tare da gwamnonin Najeriya, inji rahoton Punch.
Matsalolin Najeriya Sun Fi Karfin Tsoho Dan Shekara 70, Inji Matashin Dan Takara
A wani labarin na daban kuma, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Accord Farfesa Chris Imulomen ya bayyana cewa, kalubalen da Najeriya ke fuskanta sun fi karfin shugaba mai shekarun da suka 70 wajen warware su, rahoton jaridar The Guardian.
A cewar farfesan, Najeriya na bukatar matashi mai jini a jika dake kan ganiyar kuruciya domin ba da jininsa wajen nemo mafita ga kasar.
Ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da jam'iyyarsu ta gudanar a jihar Kano, inda yace babbar matsalar Najeriya rarrabuwar kai ne.
Asali: Legit.ng