Buhari Da Osinbajo Za Su Kashe N11.92bn Wajen Cin Abinci Da Zirga-Zirga

Buhari Da Osinbajo Za Su Kashe N11.92bn Wajen Cin Abinci Da Zirga-Zirga

  • Bayanan kudin da aka ware don tafiye-tafiyen shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo sun fito
  • Hakazalika, kudin da shugabannin na Najeriya za su kashe a fannin abinci da goge wuya shi ma ya fito fili
  • Kasafin kudin 2023 mai zuwa na nuni da cewa, ofishin Buhari da mataimakinsa kadai za su kashe N11.92bn a fannin tafiye-tafiye da cin abinci

Bincike ya nuna cewa, kasafin kudin 2023 da shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a makon jiya ya bayyana adadin kudaden da ofishinsa da na mataimakinsa za su ci a fannin tafiya da abinci kadai ya zarce N11.92bn a shekarar.

Tafiye-tafiyen da ake nufi anan na cikin gida ne da wajen kasa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kudaden da su Buhari za su kashe a cin abinci da hawa jirgi
Buhari Da Osinbajo Za Su Kashe N11.92bn Wajen Cin Abinci Da Zirga-Zirga | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jaridar Punch a yau Lahadi 9 ga watan Oktoba ta bayyana cewa, an ware N1.58bn domin kula da lafiyar jiragen sama, yayin da aka ware N1.60bn domin gyara injunan jiragen Gulfstream GV da CL605.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

A bangaren majalisun kasa, an ware N100bn domin ayyukan mazabu, kamar yadda ya zo a kasafin da Buhari ya gabatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fashin baki

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, fashin bakin kasafin kudin ya nuna cewa, an ware N2.49bn ga shugaban kasa kadai domin zirga-zirga a ciki da wajen kasar nan.

Mataimakinsa kuwa, zai kone akalla N846.61m duk dai a zirga-zirgar da zai yi zuwa wasu kasashen waje da ma cikin gida Najeriya.

Kudin man jiragen da za a yi zirga-zirga dasu kadai ya kai N250m, siyan kayayyakin kula da kuma kariya ga jiragen kuwa zai ci kusan N1.50bn yayin da za a kashe N650m ga sabon filin jirgin sama mai saukar ungulun tafi da gidanka.

Bugu da kari, N36.15m za su gangara ne a matsayin kudaden da bankuna za su ja a matsayin kudin cajin hada-hadar cirewa da tura kudin kasafin na fannin jirage.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

A bangare guda, jirage 10 da su Buhari ke hawa za su ci akalla N180m da sunan inshora.

Jiragen goma sun hada da:

  1. Boeing Business Jet (Boeing 737-800 ko kuma a ce NAF 001)
  2. Gulfstream 550 guda 1
  3. Gulfstream V (Gulfstream 500) guda 1
  4. Falcons 7X guda biyu
  5. Hawker Siddeley 4000 guda 1
  6. AgustaWestland AW 139 guda biyu
  7. AgustaWestland AW 101 guda biyu

Kasafin kudin abincin Buhari da Osinbajo

Kamar yadda yazo a kasafin kudin, kayayyakin abinci da goge wuya na shugaban kasa da mataimakinsa zai ci akalla N508.71m.

Shugaba Buhari zai ci abincin N331.79m yayin da mataimakinsa Osinbajo zai ci N176.92m.

Idan aka yi duba cikin tsanaki, akwai karin zunzurutun kudi N750m daga kasafin kudin da Buhari ya gabatar a bara.

Gwamnan Bauchi Ya Siffanta Tsohon Shugaban Najeriya Jonathan Da Shugaban Kirki

A wani labarin, gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya siffanta tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da shugaba mafi nagarta da Najeriya ta taba yi.

Kara karanta wannan

Kasafin Ƙudi: Naira Biliyan 3.34 Buhari da Osinbanjo zasu kashe a tafiye-tafiye a 2023

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da Jonathan ya ziyarce shi a Bauchi don yi masa ta'aziyyar rasuwar dan uwansa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A cewarsa:

"Kai ne dai abu mafi kyau da ya taba faruwa a kasar da ake kira Najeriya. Aikinka tukuru da sadaukarwarka ne suka sa Najeriya ta girma fiye da yadda ka same ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel