Jerin Jihohi 12 da Manyan Jam’iyyu ba za su shiga Takarar Gwamna a Zaben 2023 ba

Jerin Jihohi 12 da Manyan Jam’iyyu ba za su shiga Takarar Gwamna a Zaben 2023 ba

  • Jam’iyyar APC ta samu kanta cikin tsaka-mai-wuya a Akwa-Ibom domin ba za ta shiga zaben Gwamna ba
  • Jerin sunayen masu shiga zabe da INEC ta fitar ya nuna PDP da LP ba su da ‘yan takarar gwamna a Ogun
  • Sauran jihohin da rikicin takara ya jawowa jam’iyyu cikas sun kunshi Ebonyi, Ogun, Enugu sai Ribas

Abuja - Rigingimu da ake fama da su a kotu sun yi sanadiyyar da wasu jam’iyyu ba su da ‘dan takarar gwamnan jihohi a zaben da za ayi a 2023.

Kamar yadda Punch ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, jihohin da ake rigimar takara sun hada da Ebonyi, Akwa-Ibom, Enugu, Ribas, da kuma Ogun.

Sunayen ‘yan takaran da hukumar INEC ta fitar ya nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki ba za ta shiga zaben sabon gwamna a jihar Akwa Ibom ba.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotu Ya Nuna APC ba ta da ‘Dan Takara ko Daya a 2023 Inji Kakakin Atiku

A sunayen ‘yan takaran da aka saki babu labarin Akanimo Udofia wanda wani bangare na jam’iyyar APC suka tsaida a matsayin ‘dan takara.

Rahoton Punch yace jam’iyyun PRP, YPP da APGA ba su da wanda za iyi masu takara a Gombe, amma an kawo sunayen ‘yan takaran APC, PDP da NNPP.

A Jigawa kuwa, AAC, APM, APP da ZLP ba za su shiga zaben sabon gwamna da za a shirya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yan PDP
Magoya bayan PDP a Ogun Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Jam’iyyar LP ta gamu da babban kalubale a Kaduna domin INEC ta cire Jonathan Asake, ta maye gurbin takararsa a 2023 da sunan Alh. Umaru Ibrahim.

Hon. Shaaban Sharada shi ne wanda aka tabbatar zai yi wa ADP takarar gwamna a jihar Kano, wannan ya kawo karshen rikicin da ake yi da Nasiru Koguna.

The Cable tace gaba daya dai akwai jam’iyyu 18 da za su shiga zaben gwamnoni, sun tsaida mutane 837 a matsayin ‘yan takarar gwamna da mataimakansu.

Kara karanta wannan

Iyorchia Ayu Ya Dawo da Zafinsa, Ya Bukaci Ayi Bincike Kan Shugabannin Jam’iyya

Babu PDP a Ogun

Mun kawo maku rahoto a baya cewa PDP ba ta da ‘dan takara a jihar Ogun. Haka abin yake da jam’iyyun adawa na APGA, YPP, ZLP sai kuma LP.

A jihar ta Ogun, mutane sun shigar da kara a kan wanda ya lashe tikitin PDP, Ladi Adebutu, dukkaninsu suna kalabulantar takaran da ya samu.

Segun Showunmi, Jimi Lawal, Taiwo Olabode Idris, Kehinde Akala da Alhaji Ayinde Monsuru suna shari’a da ‘dan siyasar yanzu haka a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel