Hukuncin Kotu Ya Nuna APC ba ta da ‘Dan Takara ko Daya a 2023 Inji Kakakin Atiku

Hukuncin Kotu Ya Nuna APC ba ta da ‘Dan Takara ko Daya a 2023 Inji Kakakin Atiku

  • Daniel Bwala yana ganin APC ba za ta samu damar shiga kowane irin zabe da za a shirya a 2023 ba
  • Kakakin na kwamitin yakin zaben Atiku Abubakar presidential campaign ya kawo dalilin fadan haka
  • Bwala yace hukuncin da aka zartar a kan takarar Isiaka Oyetola ya jefa APC a tsaka-mai-wuya

Abuja - Daniel Bwala wanda yana cikin Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya yi magana a kan wani shari’a da kotun tarayya tayi.

Daniel Bwala yace hukuncin da Alkali ya zartar a kan Isiaka Oyetola da mataimakinsa, Benedict Alabi ya nuna APC ba za ta shiga takara ba.

Mai shari’a Emeka Nwite ya ruguza takarar Gwamnan Osun watau Isiaka Oyetola da mataimakinsa saboda jam’iyya ba ta bi doka wajen tsaida su ba.

Kara karanta wannan

INEC Ta Saki Sunayen Karshe na ‘Yan Takara, Babu ‘Yan Jam’iyyar PDP da LP a Ogun

Wannan shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/468/2022 ta nakasa APC bisa la’akari da cewa Mai Mala Buni ya gabatar da sunan ‘yan takara ga hukumar INEC.

An ruguzawa APC lissafi?

Da yake magana a kan wannan hukunci, Bwala wanda shi ma Lauya ne wanda ya san harkar shari’a, yace hukuncin ya rusa duk takarar wani ‘dan APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai magana a madadin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP yake magana a Twitter yana nuna jam’iyya mai mulki ba za ta shiga zabe ba.

“Idan aka yi la’akari da hukuncin kotun tarayya da ta soke takarar Gwamna Oyetola bisa cewa shugaban APC da ke ofis a lokacin bai da hurumi a doka
Hakan yana nufin APC BA TA DA ‘YAN TAKARA A DUKA ZABEN GWAMNONI, NA TARAYYA DA NA MAJALISUN DOKOKI A KASAR NAN.”

Kara karanta wannan

Allah Muke Roko Ya Bamu Mafi Alheri Tsakanin Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso - Sarkin Hausawan Awka

- Daniel Bwala

Rububin kujeru 1400

Za a gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 28 da wa’adin gwamnonin zai cika a watan Mayun 2023. Jam’iyya kusan 20 ne suka tsaida ‘yan takara a zaben.

A zaben majalisun dokoki, APC tana sa ran karawa da sauran jam’iyyu wajen neman kujeru 993.

Haka zalika za a fafata wajen neman kujerar shugaban kasa, Sanatoci 109 da ‘yan majalisun wakilai, wanda Bwala yana ganin duk APC ba za ta shiga ba.

Hukuncin ba zai zauna ba

Mr Felix Morka wanda ke magana da yawun bakin jam’iyyar APC na kasa yace kotun daukaka kara za ta canza hukuncin da aka zartar a makon da ya wuce.

An rahoto Felix Morka yana cewa Emeka Nwite ya tafka kuskure a hukuncinsa na cewa a doka, Gwamna mai-ci ba zai iya jagorantar lamarin jam'iyya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng