Kano Central: Kwankwaso Ya Magantu Kan Karar Da NNPP Ta Shigar Da INEC Saboda Kin Yarda Da Canjin Shekarau
- Jam'iyyar New Nigeria People Party, (NNPP) mai kayan marmari ta shigar da hukumar zabe INEC kotu kan rashin karbar dan takarar Kano Central
- Jamiyyar ta NNPP ta bukaci a canja sunan tsohon dan takarar Kano Central din, Ibrahim Shekarau ne saboda ya koma PDP
- A bangarenta, INEC ta ce ta ki yarda da maye sunan Shekarau da Rufai Hanga ne saboda tsohon gwamnan na Kano bai sanar da ita a hukumance ya fita daga NNPP ba
Kano - Jam'iyyar NNPP ta yi karar hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, kan rashin ba wa jam'iyyar dama ta bada sunan dan takarar sanata na Kano Central a zaben 2023, Premium Times ta rahoto.
Ainihin dan takarar, Ibrahim Shekarau, ya fita daga jam'iyyar ya koma PDP, saboda rashin jituwa tsakaninsa da dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, Rabiu Kwankwaso.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shekarau bai sanar da mu ya bar NNPP ba - INEC
Hukumar INEC, yayin bada dalilinta ta ce Mr Shekarau, tsohon gwamnan Kano bai riga ya sanar da ita a hukumance cewa ya bar NNPP ba don haka bisa dokar zabe, ba za ta iya maye gurbinsa da wani ba.
Kwankwaso, a hirar da ya yi da gidan Rediyo na Deutsche Welle Hausa a ranar Laraba, ya ce hukumar zaben ta ki amincewa ta maye gurbin Shekarau da sabon dan takarar, Rufa'i Hanga, da jam'iyyar ta mika bayan sauya shekarsa.
Rashin amincewar Kwankwaso
Yayin hirar da aka yi da shi, Kwankwaso ya ce yana tunanin idan NNPP ta ce zaben sanatan Kano Central, shin INEC za ta sanar da Shekarau a matsayin halastaccen wanda aka zaba?
Zaben 2023: Wasu Yan APC Suna Guna-Guni Kan Rashin Saka Sunan Tallen, Binani Da Wasu A Kungiyar Kamfen Na Mata
Kwankwason ya ce:
"Mun yi sabon zaben fidda gwani kuma mun zabi Rufa'i Sani Hanga, a matsayin wanda zai maye gurbi kuma idan INEC za ta mana adalci, bisa kundin tsarin mulki, lokacin canja dan takara bai wuce ba.
"Mun kai kara a kotu saboda INEC ba ta fahimci lamarin ba. Kotu za ta fahimtar da su."
2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu
A wani rahoton, mutum hudu cikin wadanda za su yi takara a zaben 2023 karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a Jihar Osun, a ranar Laraba sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Bola Tinubu.
Yan takarar, Clement Bamigbola, dan takarar sanata na Osun Central; Bolaji Akinyode, dan takarar sanata na Osun West; Olalekan Fabayo da Oluwaseyi Ajayi, yan takarar majalisar tarayya na Boluwaduro/Ifedayo/Ila, da Ijesa South kamar yadda aka jero.
Asali: Legit.ng