An Fallasa ‘Yar Majalisa a Kotu, Makaranta ba ta san da Zaman Satifiket dinta ba

An Fallasa ‘Yar Majalisa a Kotu, Makaranta ba ta san da Zaman Satifiket dinta ba

  • An shigar da karar Mosunmola Sangodara a kotu, ana neman hana ta tsayawa takara a zaben badi
  • Jam’iyyar APC ta tsaida Mosunmola Sangodara a matsayin ‘yar takarar Surulure II a majalisar dokoki
  • Idan ‘yar siyasa tayi rashin sa’a, za a iya haramta mata shiga takara a 2023 saboda karyar satifikey

Lagos - Mataimakin Magatakardar Kwalejin Fasaha ta Yaba, Olufunmi Dada ya bayyana a kotun tarayya na Legas kan shari’ar Mosunmola Sangodara.

This Day tace Olufunmi Dada ya bada shaida a shari’ar da ake yi da Mosunmola Sangodara mai neman wakiltar Surulere a majalisar dokokin jihar Legas.

Dada ya yi wa Mai shari’a Nicholas Oweibo bayanin abin da ya sani a kan Mosunmola Sangodara, wanda ke ikirarin tayi karatunta a makarantarsu.

Da yake bayani, ma’aikacin na Yaba College of Technology yace Sangodara ba ta cikin wadanda suka halarci makarantar, har ta kai ga samun shaidar HND.

Kara karanta wannan

Iyorchia Ayu Ya Dawo da Zafinsa, Ya Bukaci Ayi Bincike Kan Shugabannin Jam’iyya

Ma’aikacin ya kawo jerin sunayen daliban da aka yaye a makarantar da ke Legas tsakanin shekarar 1992 da 1997, kuma ba a samu sunan ‘yar siyasar ba.

Lauya ya nemi abin suka

Lauyan da ya tsayawa wanda ake zargi, Adebisi Oridare ya nemi jin abin da ya sa bai iya kawo sunayen daliban da aka yaye a kakar 1995/1996 ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yar Majalisa
Mosunmola Sangodara da Desmond Eliot Hoto: @hsangodara
Asali: Twitter

Da yake bada amsa, magatakardan yace a wancan lokaci an hada daliban da suka kammala a1994/1995 da na 1995/1996, an yaye su a lokaci daya.

Sahara Reporters tace Dr. Kemi Pinheiro SAN shi ne Lauyan da ya jagoranci Dada wajen bada shaida a babban kotun tarayyan mai zama a Legas.

Bugu da kari, Dada ya fadawa Alkali cewa akwai alamar tambaya a game da takardar kauracewa bautar kasa da ‘yar siyasar take ikirarin NYSC ta ba ta.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a Sun Maka IGP da CMD Kotu, Sun Bukaci Alkali Ya Jefa su Kurkuku

Za a cigaba da zama a yau

Alkali Oweibo ya karbi duka shaidar da aka bada domin ayi amfani da su a shari’ar. Baya ga haka, ya umarci hukumar WAEC suka wanda zai bada shaida.

A yau Laraba ake sa ran za a cigaba da sauraron shari’ar da ake yi da Sangodara. Abin da lauyoyin masu kara suke so shi ne a hana ta shiga takarar majalisa.

S.O. Ibrahim a matsayinsa na lauyan INEC, ya fadawa kotu cewa adalci suke nema ayi a shari’ar.

CONUA dabam da ASUU

Bayan samun rajistar Gwamnatin tarayya, mun ji labari Shugaban Congress of Nigerian University Academics ya fadi manufofinsu na gyara jami’o’i.

Shugaban CONUA yace za suyi kokarin kawo mafita a jami’o’i domin dalibai da iyaye suke shan wahala a yajin aikin da ASUU ta dade tana yi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel