Kan ku ake ji: Atiku Abubakar Ya Maida martani ga 'Yan PDP da Ake Rikici da su

Kan ku ake ji: Atiku Abubakar Ya Maida martani ga 'Yan PDP da Ake Rikici da su

  • Kwamitin takarar Atiku Abubakar/Ifeanyi Okowa yace akwatin zaben 2023 kurum yake hange yanzu
  • Daniel Bwala wanda shi ne kakakin Kwamitin yakin zaben yace babu wani abin da zai janye masu hankali
  • Bwala ya yi raddi ga wani jagora a jam’iyyar PDP da aka ji har yanzu yana maganar a tsige Iyorchia Ayu

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar/Ifeanyi Okowa yace babu abin da yake hari illa zaben shugaban kasa mai zuwa na 2023.

Daily Trust tace Mista Daniel Bwala wanda yana cikin masu magana da yawun bakin kwamitin ya yi raddi a kan wasu zargi da ake jefa masu.

A wani jawabi da ya fitar, Daniel Bwala yace jirgin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya daina waiwaye, ya sa batun zaben 2023 a gabansa.

Jawabin martani ne ga Cif Chinemerem Madu, daya daga cikin ‘yan majalisar koli ta PDP, wanda ake cewa yana kiran a tunbuke shugaban jam'iyya.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku Zai Bi Wajen Maganin Akidar Biyafara Da Tayi Shekara da Shekaru

Bwala yace ana yunkurin jawo rudani da jawabin Chinemerem Madu a lokacin da jam’iyyar da ‘ya ‘yanta suke kokarin ceto al'ummar kasar nan.

Jawabin Daniel Bwala:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“An rantsar da ‘yan kwamtin yakin neman zabenmu yau wajen kaddamar da littatafan ‘dan takaranmu, Mai girma, Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar
Atiku Abubakar yana kamfe
Asali: Twitter

“Mun shirya fara yakin neman zabe a yau, shiyasa ake yunkurin gurgunta kokarin da muke yi.
“Bikin kaddamar da kamfe din ya jawo dinbin jama’an da sauran mutanen Najeriya da suka yi azama wajen ganin mun samu nasara.

- Daniel Bwala

Ba wannan ne a gabanmu ba

"A matsayinmu na jam’iyya, ka da ka raba daya biyu, mun rabu da duk wani jan hankali na babu gaira babu dalili, muna hangen gabanmu."

- Daniel Bwala

Atiku ya fi kowane 'dan takara tanadi

An rahoto kakakin kwamitin yakin neman zaben yace jam’iyyar PDP mai adawa ta tsara yadda za ta gyara Najeriya idan ta karbi shugabanci.

Kara karanta wannan

An Gano Yadda Tinubu Ya Assasa Rikicin APC kan Kwamitin Yakin Neman Zabensa

Sannan Bwala yake cewa manufofin tattalin arzikin Atiku Abubakar shi ne ya fi na kowane ‘dan takara kyau kamar yadda masana suka fada.

Zan kawo karshen Biyafara - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma 'dan takaran 2023, yace zai yi kokari wajen ragewa gwamnatin tarayya iko, ya karawa jihohi karfi.

Shekaru fiye da 50 ana fama da batun raba Najeriya. An samu labari gwamnatin Atiku ta bayyana yadda wannan akida za ta zama tsohon tarihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel