Kai Tsaye: Wike Ya Fara Zaman Tonon Silili Kan Jam'iyyar PDP

Kai Tsaye: Wike Ya Fara Zaman Tonon Silili Kan Jam'iyyar PDP

Rana Bata Karya, Gwamnan jihar RIvers ta hau minbarin fara tonon silili kan wasu jiga-jigan jam'iyyar Peoples's Democratic Party PDP a yau Juma'a.

Jiya Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya lashi takobin tona asirin wasu shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) masu ikirarin su iyayen jam'iyyar ne.

Idan yan Najeriya suka ji abinda ke faruwa a PDP, zasu yi mamaki

Nyesom Wike ya bayyana cewa idan ya fadi irin abubuwan dake faruwa a jam'iyyar PDP dake ikirarin son komawa gadon mulki zasu yi mamaki.

A cewarsa:

"Shin zan zo gaban gidajen talabijin in fadi abinda ban sani bane. Idan yan Najeriya suka san abinda ke faruwa a jam'iyyar dake son komawa mulki zasu sha mamaki."

Masu baiwa Atiku shawara basu son shi, Wike

Nyesom Wike ya bayyana cewa masu baiwa dan takaran shugaban kasa Atiku Abubakar shawara basu son shi.

Wike yace don Buhari ya lashe zabe a 2015 da 2019 duk da bai ci zaben jihar Rivers ba, Atiku ba zai iya ba.

Wike yace:

"Buhari ya lashe Legas, ya lashe Kano. shin Atiku zai iya lashe Legas? Zai iya lashe Kano."
"Masu baiwa dan takaranmu shawara basu son sa. Akwai daya a Edo"

Akwai masu goyon bayan PDP a fadar shugaban kasa saboda mulki ya koma Arewa

Nyesom Wike ya bayyana cewa akwai wasu a fadar shugaban kasa Buhari masu goyon bayan dan takaran kujeran shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Yace suna hakan ne saboda kada mulki ya koma kudu idan Tinubu yaci, gwanda Atiku yaci mulki ya tsaya a Arewa.

Shugaban jam'iyyar PDP Iyorchia Ayu, barawo ne

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce shugaban uwar jam'iyyar PDP Iyorchia Ayu barawo ne kuma yana amsan cin hanci da rashawa.

Wike yace idan Ayu ya isa ya karyata cewa bai tafi Legas ya karbi makudan kudi hannun wani dan takaran kujeran shugaban kasa ba.

Wike yace:

"Ayu babban dan rashawa ne. Bari in fada muku daya. Ayu ya karbi kudi hannun wani dan takara a Legas."
"Ba wajen gwamnatin Legas nike nufi ba, amma a Legas yake ya karbi kudin."

Ayu Da kansa yace Idan Atiku Yaci zaben fidda gwani zai yi murabus

Wike ya bayyana cewa sai shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, da kansa ya fadawa duniya zai ajiye kujerar idan Atiku Abubakar ya ci zaben fidda gwani.

A cewarsa, babu wanda ya tilasta Ayu fadin haka, da kansa yayi.

A cewarsa:

"Ayu da kansa yace zai yi murabus. Wa ya tilasta shi fadin haka? Saboda ya san abinda ya kamata ne."
"A lokacin Ayu kullum sai ya kirani a waya yana godiya."
Online view pixel