Saura ni: Yadda Aka Doke Ahmad Lawan a Kotu, Hadimin Buhari Yana Sa Ran Takara

Saura ni: Yadda Aka Doke Ahmad Lawan a Kotu, Hadimin Buhari Yana Sa Ran Takara

  • Bashir Ahmaad ya yi magana bayan ya samu labarin nasar Hon. Bachir Machina a kotu
  • Alkali ya yanke hukunci cewa Machina ne zai yi wa APC takarar Sanatan Yobe ta Arewa
  • Bashir Ahmaad ya nuna yana sa ran Alkali ya ba shi tikitin APC na Gaya/Ajingi/Albasu

Abuja - Nasarar da Bachir Machina ya samu a kotu, ta karawa Bashir Ahmaad kwarin gwiwa a yakin samun takara a zabe mai zuwa na 2023.

Bashir Ahmaad ya nemi tikitin ‘dan majalisar tarayya na mazabar Gaya/Ajingi/Albasu, amma ya sha kashi a zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC.

Da ya samu labarin Hon. Bachir Machina ya yi galaba a kotu a kan Sanata Ahmad Lawan, sai ya fito shafin Facebook, yana tofa albarkacin bakinsa.

Kara karanta wannan

Pantami Ya Jagoranci Najeriya da Afrika Sun Samu Gagarumar Nasara a Duniya

Hadimin shugaban Najeriyan ya rubuta:

“Bashir Machina na Yobe, sauran Bashir Ahmad na Kano, da yardar Allah.”

- Bashir Ahmaad

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan yana nufin yadda Alkali ya tabbatar da Bashir Machina a matsayin ‘dan takaran Sanatan Yobe ta Arewa a APC, shi ma Ahmaad zai kai labari.

Matashin ‘dan siyasar yake cewa da yardar Allah shi ma za a ayyana shi a matsayin ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Gaya, Ajingi da Albasu.

Bashir Ahmaad
Bashir Ahmaad Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Bashir Ahmaad v Mahmud Gaya

Ahmaad mai shekara 31 ya tabbatar da cewa yana shari’a da Honarabul Mahmud Gaya wanda jam’iyyar APC ta sake ba tikitin majalisa a zaben 2023.

Da yake maida martani a shafin na sa, Bashir Ahmaad ya shaidawa wani Yakubu Musa yana shari’a a kan neman takararsa a jam’iyyar APC mai mulki.

Duk da bai yi dogon bayani ba, mai ba shugaban kasa shawaran yake cewa su na kotu, kuma ya tabbatar da cewa zuwa yanzu yana ta samun nasara.

Kara karanta wannan

Abin da Zai Jawo Kotu Ta Iya Hana Bola Tinubu da Sauran ‘Yan APC Tsayawa Takara

Fatan alheri

Jama’a da ke bibiyan ‘dan siyasar a dandalin Facebook sun yi masa fatan alheri a shari’ar da za ayi. A gefe guda kuma an samu masu yi masa adawa.

Allah ya amsa Bashir Ahmad.

- Abdul Danja

Wani 'Dan adawa ya rubuta:

Allah ya sa su ba ka takarar yadda zamu samu saukin kayar da ku

- Ibrahim Umar Bari

Shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Prince Muhammad Kadade Suleiman ya ba takwaran na sa shawarar ya yi hakuri da maganar zuwa gaban kuliya.

Honourable ayi hakuri

- Prince Muhammad Kadade Suleiman

Wai har yanzu baka hakura ba kenan?

- Yusuf M. Nasir

Takarar Tinubu a APC

A baya kun samu labari cewa Bola Tinubu mai neman takarar shugaban kasar Najeriya a 2023 a inuwar APC zai fadada kwamitin kamfe dinsa.

Ana tunani za a karo mutane 2000 da za su taya APC yakin neman takara, majalisar kamfe za ta saurari Gwamnoni da 'yan APC NWC da ke yin korafi.

Kara karanta wannan

Na Hannun Daman Gwamnan Arewa Da Daruruwan Magoya Baya Sun Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng