An fara kamfe: Atiku Ya Dura Abuja, Tinubu Ya Tafi Landan, Peter Obi Ya Dakata Tukun

An fara kamfe: Atiku Ya Dura Abuja, Tinubu Ya Tafi Landan, Peter Obi Ya Dakata Tukun

  • ‘Dan takaran shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya kama hanyar Abuja da nufin ya fara kamfe
  • Alhaji Atiku Abubakar da Gwamnonin jam’iyyar PDP za su kaddamar da kwamitin yakin neman zabe
  • Jam’iyyun LP da APC sun dakatar da fara yakin zaben shugaban kasa, ba a san yaushe za su soma ba

Abuja - A ranar Laraba, 28 ga watan Satumban 2022 za a kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP mai adawa.

Punch tace ‘dan takaran PDP a 2023, Atiku Abubakar ya isa garin Abuja tare da wasu gwamnonin jihohi da nufin a shiga kamfe da aka fara daga yau.

Ana sa rai Atiku Abubakar da ‘yan kwamitin yakin neman takaran za su hallara a babban dakin taro na ICC a garin Abuja domin bikin rantsarwar.

Kara karanta wannan

Kwamitin kamfe Ya Yi Martani ga Gwamnonin APC da Suka yi Fushi da Bola Tinubu

Ya za ayi da Wike a PDP?

Jam’iyyar PDP za ta fara aikin neman zabe ba tare da Gwamna Nyesom Wike da mutanensa ba. Dr. Bukola Saraki yana ta kokarin shawo kansu.

‘Yan bangaren PDP da ke tare da Wike wajen yakar takarar Atiku sun hada da tsofaffi da gwamnoni masu-ci da tsofaffin ‘yan majalisa da Ministoci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ina Tinubu suka shiga?

A lokacin da Atiku yake shirin kaddamar da kwamtin neman zabe, ‘dan takaran jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya tafi kasar waje.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a Enugu Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Jam’iyyar APC ta dakatar da soma aikin kamfe, sannan tace za ta fadada kwamitin yakin zaben shugaban kasa wanda yake kunshe da mutum 422.

Obi: A saurare mu - Arabambi Abayomi

Rahoton ya nuna shi ma Peter Obi mai neman mulkin Najeriya a zaben 2023 a karkashin LP ba zai fara yakin neman zaben shugaban kasa a yau ba.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Za Ta Fara Yakin Neman Zabe da Addu’o’in Musamman na Neman Sa’a

Arabambi Abayomi wanda jigo ne a tafiyar Obi, bai fadi ranar da za su soma kamfe ba, amma yace a ranar da suka fara yakin zabe, za su fitar da manufofinsu.

Majiyarmu ta shaida mana cewa a makon nan ake sa rai ‘dan takaran NNPP, Rabiu Kwankwaso zai ziyarci jihar Filato domin bude ofishin jam’iyyarsu.

Har yanzu Sanata Rabiu Kwankwaso bai fito da manufofinsa ba, kuma ba a ji labarin ya kaddamar da ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ba.

Dattawan Arewa za su tsaida 'dan takara

Kun ji labari Northern Elders Forum ta Dattawan Arewa tace kafin ta yanke shawara tsakanin 'yan takaran na 2023, sai ta zauna da kowanensu tukuna.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed yace an gama yin irin kuskuren da aka yi a baya, duk aka taru aka ce ‘Sai Baba’ a zaben 2015, a karshe bai yi masu rana ba.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Peter Obi Na Kara Yin Suna Da Karfi, Babban Jigon APC Ya Yi Hasashe Mai Karfi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng