'Dan takaran 2023 Ya yi Sabon Zama da Obasanjo, An yi Kus-kus 'a kan batun kasa'

'Dan takaran 2023 Ya yi Sabon Zama da Obasanjo, An yi Kus-kus 'a kan batun kasa'

  • ‘Dan takaran Shugabancin Najeriya a jam’iyyar hamayya ta LP ya yi kus-kus da Cif Olusegun Obasanjo
  • Kwanaki Olusegun Obasanjo ya hadu da Obi a Landan, sannan sun taba yin zama irin wannan a Abeokuta
  • A ‘yan kwanakin nan, Obi ya ziyarci Obasanjo, Janar Abdulsalami Abubakar da Janar Ibrahim Babangida

Ogun - Peter Obi mai neman zama shugaban Najeriya a 2023 a karkashin jam’iyyar Labour Party (LP) ya hadu da Cif Olusegun Obasanjo.

Mista Peter Obi ya wallafa hotunan haduwarsa da Olusegun Obasanjo a shafinsa na Twitter a yammacin Litinin, 26 ga watan Satumba, 2022.

‘Dan takaran ya nuna godiyarsa ga Mai girma Obasanjo ga damar da ya ba shi na su zauna su tattauna a kan batutuwan da suka shafi Najeriya.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

The Cable ta ce wannan ne karo na biyu da shugabannin suka hadu a ‘yan makonni. Kwanakin baya an gan su tare a Landan da ke kasar Ingila.

Har ila yau, Obi da abokin takararsa a LP, Yusuf Datti Baba-Ahmed sun taba kai wa tsohon shugaban kasar irin wannan ziyara a gidansa.

Me aka tattauna a wannan zama?

Ana zargin tsohon shugaban na Najeriya yana cikin masu goyon bayan takarar Obi a zaben 2023. Obasanjo ya yi fiye da shekara 10 yana mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Peter Obi
Peter Obi tare da Olusegun Obasanjo Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Daily Trust ta kawo rahoto haduwar, amma ba ta iya fadin abin da aka tattauna yayin da ‘dan takaran shugaban kasar ya sa labule da dattijon ba.

Abin da Peter Obi ya fada

"Ina mai matukar godiya ga damar yin zama domin tattaunawa da kyau da Olusegun Obasanjo yau a kan batutuwan kasa.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Hallaka Jagororin ‘Yan Bindiga da Wasu Miyagu Barkatai a Katsina da Zamfara

Kamar yadda aka saba, zaman na mu cike yake da hangen nesa da karfafawa."

- Peter Obi

Obi yana bin manyan kasa

Haduwar Obi da Obasanjo ta zo ne kwana daya bayan an gan shi a gidan Janar Abdulsalami Abubakar (Mai ritaya) a garin Minna, a jihar Neja.

Har ila yau, ‘dan takaran ya zauna da Janar Ibrahim Badamasi Babangida (Mai ritaya). Har zuwa yanzu ba mu da masaniyar wainar da aka toya.

Tinubu sun bar Najeriya

A baya an ji labari Bola Tinubu da Abokin takararsa, Kashim Shettima sun lula Landan. Bisa dukkan alamu 'yan takaran za su huta ne a ketare.

‘Yan takaran sun yi tafiya ne ana daf da soma kamfe a Najeriya. Bayo Onanuga yace a watan Oktoba Tinubu zai dawo gida, ya fara yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng