Akwai Sanatan PDP, amma babu Yemi Osinbajo a Kwamitin yakin zaben Tinubu
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo bai cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben APC a 2023
Amma akwai sunan sauran wadanda suka yi takara da Bola Tinubu wajen neman tikiti irinsu Rotimi Amaechi
Babu tsohon Ministan sadarwa da tsohon shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara a kwamitin
Abuja - Legit.ng Hausa ta bibiyi jerin sunayen da jam’iyyar APC ta fitar na ‘yan kwamitin kamfe a 2023, ta fahimci babu sunan Farfesa Yemi Osinbajo.
Mai girma mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo bai samu shiga cikin mutum 422 da za su yi wa Bola Tinubu yakin neman mulki ba.
Osinbajo yana cikin manyan makusantan ‘dan takaran tun 1999. Daga baya alakarsu ta canza, har suka yi takara da juna a wajen neman tikitin jam’iyya.
Daily Trust tace baya ga Osinbajo, wani suna da aka gani a wannan dogon kwamiti shi ne tsohon Ministan sufurin tarayya, Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar dai Farfesa Osinbajo, shi ma Rotimi Amaechi ya yi takara da tsohon gwamnan Legas a zaben tsaida gwani na APC, amma bai iya yin nasara ba.
Chimoroke Nnamani ya zama 'Dan APC?
Kusan abin da ya fi bada mamaki shi ne bayyana sunan Sanata Chimoroke Nnamani a jerin duk da shi Sanatan PDP ne wanda ke tare da Atiku Abubakar.
Kwanaki aka ji Nnamani yana yabon Tinubu, yana sukar magoya bayan Peter Obi. Vanguard tace Sanatan na jihar Enugu ya samu shiga kwamitin.
Wani wanda fitowarsa sunansa ya mutane mamaki shi ne Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola. Ana ganin babu jituwa tsakaninsa da Tinubu.
Jaridar tace Adebayo Shittu bai shiga cikin ‘yan kwamitin kamfe ba, duk da gudumuwar da yake ta badawa wajen ganin Tinubu ya samu mulki.
An fahimci babu sunan tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara, wanda shi da Babachir Lawal suke neman juyawa APC baya.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya dawo daga rakiyar 'dan takaran ne tun da ya dauki Musulmi a matsayin abokin takararsa.
Abokan hamayya a zaben APC
Amma duk da haka, rahoton da muka samu yace Tinubu ya dauki wasu daga cikin wadanda suka yi takara da shi a neman tikitin shugaban kasa.
A jerin da aka fitar akwai sunan Sanata Ahmad Lawan, Chibuike Rotimi Amaechi, Ibikunle Amosun, Dr Ogbonnaya Onu da Sanata Ken Nnamani.
Har ila yau kwamitin na kunshe da Ikeobasi Mokelu, Ahmad Zani Yarima da Rochas Okorocha.
Asali: Legit.ng