Gwamna Wike Ya Fallasa Sirrin Zaman da Ya yi da su Bola Tinubu a Kasar Waje

Gwamna Wike Ya Fallasa Sirrin Zaman da Ya yi da su Bola Tinubu a Kasar Waje

  • Nyesom Wike yace a zamansa da ‘Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu, an yi masa tayin tikitin Sanata
  • Gwamnan na jihar Ribas ya fadawa ‘yan jarida, mulkin Najeriya yake nema, ba ya tafi majalisar dattawa ba
  • ‘Dan siyasar yace baya ga jam’iyyar APC, ‘Ya ‘yan LP da wasunsu suna zawarcinsa domin cin zabe

Rivers - Gwamnan jihar Ribas ya kira taron manema labarai a ranar Juma’a, 23 ga watan Satumba, 2022, inda ya yi bayanin wasu batutuwa.

Vanguard tace Mai girma Nyesom Wike ya yi bayanin yadda Asiwaju Bola Tinubu ya yi masa tayin kujerar majalisar dattawa a karkashin APC.

Bola Tinubu wanda ke neman kujerar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki ya zauna da Nyesom Wike bayan ya rasa tikitin shugaban kasa a PDP.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu

Gwamnan yace ‘dan takaran na jam’iyya mai-ci ya yi yunkurin jawo shi ya nemi Sanata a matsayin danna-kirjin rasa takarar shugaban kasa.

Sanata? A kai kasuwa - Wike

Mista Wike ya shaidawa manema labarai a babban birnin Ribas na Fatakwal cewa bai karbi tayin da tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi masa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto Gwamnan bai shirin barin-gado a 2023, yana cewa tun farko bai saye fam din Sanata ba, domin shugabancin kasa yake nema.

Nyesom Wike
Gwamnonin APC, Wike da Fayose Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

“Ban shiga takara saboda in nemi mataimakin shugaban kasa ba. Ni ba kamar sauran da ba da gaske suke yi ba ne, suka saye fam na Sanata da na shugaban kasa ba.
Shiyasa da Bola (Tinubu) ya yi mani tayin kujerar Sanata, ban karba ba. Idan ina neman mulki ne, to da sai in karbi tikitin takarar Sanata. Amma sai na ce masa a’a.

Kara karanta wannan

Ana Samun Rabuwar Kai a Kamfe Saboda Tinubu Ya Jawo Gwamna, Ya Ba Shi Mukami

- Nyesom Wike

Wike ya yabi Tinubu, yace yayi tsada

Shi ne mutum da ya yadda da adalci da gaskiya. Saboda haka abin da ake fada ba haka ba ne."

- Nyesom Wike

Baya ga Tinubu da ke APC, sauran jam’iyyu suna magana da ni, har da Labour Party, domin sun san daraja ta, da yadda zan taimaka masu wajen lashe zabe.
Amma ban karbi tayin da wadannan jam’iyyu suke yi mani ba."

- Nyesom Wike

An ji labari Bola Tinubu da mutanensa sun hadu da Gwamna Wike a birnin Landan a lokacin da ake ta rade-radin zai iya barin PDP tun da bai ci takara ba.

Tsohon Ministan ya dade yana nanata cewa bai da niyyar sauya-sheka daga jam’iyyarsu ta PDP, zai cigaba da zama ta gwabza da abokan fadansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel