Jam'iyyar APC Ta Saki Jerin Sunan Yan Kwamitin Kamfe 442, Babu Osinbajo

Jam'iyyar APC Ta Saki Jerin Sunan Yan Kwamitin Kamfe 442, Babu Osinbajo

Jam'iyyar All Progressives Congress ta saki jerin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zabenta a daren Asabar, 24 ga watan Satumba 2023.

Kwamitin mai adadin mambobi 442 ya hada da shugabannin jam'iyyar, gwamnoni, tsaffin gwamnoni, har da shugaban kasa.

Sakataren kwamitin kamfen, James Faleke, ya sakin jerin sunayen a shafinsa.

Yace:

"Muna farin cikin sanar da sunayen mambobin kwamitin kamfen APC a cikin wadannan takardu."
"Duk wanda ya ga sunansa ya garzaya hedkwatar kamfen Tinubu dake Plot 171 Herbert MacaulyWay CBD Abuja misalin karfe 12 na ranar Litinin don daukar takardar shaidar zama mamba."

An nada Shugaba Muhammadu Buhari matsayin Uban kwamitin yayinda aka nada Asiwaju Tinubu matsayin mataimakin shugaban kwamitin na 1, sannan shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu matsayin shugaban kwamitin na 2.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Tambuwal ya karbe mukamin shugaban gwamnonin Najeriya

Hakazalika an nada Gwamna Simon Lalong matsayin Dirakta Janar na kamfen yayinda aka nada Adams Oshiomole matsayin mataimakin dirakta.

Kalli jerin sunayen a nan:

Asali: Legit.ng

Online view pixel