INEC Ta Manna Sunan Shekarau a Matsayin Dan Takarar Sanatan NNPP, Duk da Sauya Sheka Zuwa PDP

INEC Ta Manna Sunan Shekarau a Matsayin Dan Takarar Sanatan NNPP, Duk da Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta cire sunayen 'yan takarar zaben 2023 mai zuwa nan ba da jimawa ba
  • Sunan Shekarau bai fito a jerin 'yan takarar da za su gwabza a karkashin jam'iyyar PDP ta su Atiku ba
  • A watan jiya ne dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya dira Kano ya karbi Shekarau zuwa jam'iyyar PDP daga NNPP

FCT, Abuja - Bayan kammala wani zama a yau Talata 20 ga watan Satumba, hukumar zabe mai kanta (INEC) ta fitar da sunayen 'yan takarar da za su gwabza a zaben 2023 mai zuwa.

Jerin da INEC ya fitar na dauke da sunaye, jam'iyyu, matakin karatu da shekarun kowane dan takara, TheCable ta ruwaito.

An bayyana bayanan dukkan 'yan takara, amma a bangaren jihar Kano, an samu tsaiko ko kuskuren wallafa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Bwacha

Shekarau ba ya cikin jerin 'yan takarar PDP, ya fito a NNPP
INEC Ta Manna Sunan Shekarau a Matsayin Dan Takarar Sanatan NNPP, Duk da Sauya Sheka Zuwa PDP | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shekarau na NNPP har yanzu, a bayanin INEC

Mallam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar jihar Kano wanda a yanzu ke wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ya fito a cikin jerin, kamar yadda INEC ta saki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

INEC ta bayyana shi a matsayin dan takarar NNPP duk da cewa ya sauya sheka zuwa PDP a watan jiya.

A bangare guda, akwai alamu da ke nuna INEC ta yi kuskure, domin kuwa Shekarau ya tura wasikar janyewa daga takara, kuma bai bayyana karbar tikitin PDP na sanata ba.

A baya mun kawo muku rahotanni kan yadda rikici ya barke tsakanin Kwankwaso da Shekarau, lamarin da ya kai ga Shekarau ya bar NNPP watanni kadan bayan shigarsa.

Shekarau dai ya zargi Kwankwaso da cin amanarsa tare da saba masa dukkan alkawuran da suka kulla a lokacin da ya shiga NNPP.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Rikici ne ya hada Shekarau da 'yan tsagin Ganduje a jam'iyyar APC, har ya bar jam'iyyar ya shiga NNPP, ga shi dai yanzu ba ya APC, ba kuma ya NNPP; ya koma PDP.

Lagon Atiku a Kebbi Ya Yi Sako-Sako, Jiga-Jigan PDP da Yawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC

A wani labarin, jam'iyyar APC a jihar Kebbi ya karbi wasu jiga-jigan siyasan da suka sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP, PM News ta ruwaito.

Daya daga jiga-jigan da suka sauya sheka akwai tsohon babban oditan PDP, Alhaji Rabi'u Sa'idu, tsohon sakateren kwamitin riko na PDP Alhaji Sirajo Ibrahim da wasu manyan mambobin PDP 15 daga unguwar Bubuce a karamar hukumar Augie ta jihar.

Sauran sun hada da Umaru Wakkala, mataimakin shugaban PDP na Bubuce; Salihu Shayi, shugaba matasan yankin; Alhaji Idi Babuce, ma'ajin jam'iyya da kuma Hamza Akilu, oditan jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel