Isa Ali Pantami Ya Yi Zarra Kan Sauran Ministoci, Gwamnati Ta Ba shi Lambar Yabo
- Gwamnatin jihar Abia ta karrama Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin Najeriya da lambar yabo
- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ci kyautar zama Ministan da ya fi kowa amfani da kafofin zamani
- An ba shi kyautar Best Performing Digital Minister for the Year 2022 a ranar tunawa da fasahohin zamani
Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na kasa, Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu lambar yabo a dalilin irin kokarin da yake yi a Najeriya.
Rahoton VON ya tabbatar da cewa Ministan ya samu kyautar “Best Performing Digital Minister for the Year 2022.” watau gwarzon Ministan zamani na 2022.
Wannan kyauta tana nufin a cikin Ministocin kasar, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya yi zarra a bangaren harkokin fasahar zamani a shekarar bana.
Hotunan Fasto Yana Raba Wa Almajirai Allo Da Kayan Karatu A Kaduna Don Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya
Gwamnatin jihar Abia ta ba Ministan wannan lambar yabo bayan la’akari da irin sauyin da ya kawo a bangaren tattalin arziki da fasahohin zamani.
Rahoton yace Darektan bincike da cigaba na hukumar NITDA na kasa, Dr. Agu Collins Agu ya karbi wannan kyauta a madadin Farfesa Isa Ibrahim Pantami.
Gwamnatin Abia tace ta karrama Ministan ne saboda kokarin da yake yi wajen ganin an koma amfani da kafofin zamani da nufin zaburar da tattalin arziki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ranar International Identity
Ofishin Mai ba gwamna shawara a kan harkar hukumar katin zama ‘dan kasa na jihar Abia sun shirya biki domin tunawa da ranar International Identity Day.
An ware irin wannan rana a Duniya domin a rungumi kafafin sadarwa na zamani da ake da su. Ministan yace ya ji dadin karbar kyautar a irin wannan rana.
A jawabinsa, Farfesa Pantami ya yabi Mai girma Gwamnan jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu a game da yunkurin da yake yin a bunkasa bangaren ICT a jiharsa.
Pantami ya cancanci yabo - Abia
Matimakin gwamnan Abia, Sir Ude Chukwu ya wakilci Gwamna a taron, inda aka ji yana yabon irin gudumuwar da Ministan tarayyar ya rika ba su a ofis.
Sir Ude Chukwu yace sun samu taimako daga Isa Ali Pantami wajen tattara bayanan mutanen jihar, ya kara da cewa Ministan ya cancanci wannan lamba.
Gaba dai...gaba dai
Kwanakin baya aka ji labari Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya samu lambar zama ‘dan kungiyar Chartered Institute of Information Security.
Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya samu wannan lamba biyo bayan wasu jarrabawowi da kungiyar tayi wa Mai girma Ministan, ya kuma yi nasara.
Asali: Legit.ng