Ministan Najeriya, Pantami Ya Ajiye Tarihi, Ya Yi Abin da Babu Wanda Ya Yi a Afrika

Ministan Najeriya, Pantami Ya Ajiye Tarihi, Ya Yi Abin da Babu Wanda Ya Yi a Afrika

  • Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya samu shaidar CIISec bayan yi masa jarrabawowi da gwaji
  • Ministan sadarwan yana da shaidar zama kwararre kan harkar tsare kafofin yanar gizo
  • Pantami ne mutumin farko a Afrika da ya samu wannan dama, mutum 89 ke da CIISec

Farfesa - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya samu lambar zama ‘dan kungiyar Chartered Institute of Information Security.

Vanguard ta kawo rahoto cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya samu wannan lamba ne biyo bayan wasu jarrabawowi da kungiyar tayi wa Mai girma Minista.

Kamar yadda cibiyar mai bada lambar girman ta bayyana, ana bada CIISec ne ga jagororin da suka yi fice wajen harkar tsaron bayanai da kafofin yanar gizo a Duniya.

Kara karanta wannan

Babu Nadamar Komai Saboda Tunbuke Ni, Kuma Ba Zan Yi Shiru Ba Inji Sanusi II

Legit.ng ta fahimci Isa Ibrahim wanda aka fi sani da Pantami ya samu shaidar CIISec, hakan na nufin ya zama cikakken kwararren ‘dan kungiyar tsaron yanar gizo.

Pantami ya bi sahun mutane 89

Rahoton Sun yace Ministan tarayyan ya zama mutum na 89 a Duniya da ke da wannan shaida, na farko a fadin nahiyar Afrika da ya taba samun shaidar CIISec.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutum yana samun CIISec ne idan ya yi fice a bangaren tsaron yanar gizo, baya ga haka ya nuna kokari wajen bunkasa wannan harka da yanzu ake ci da shi a ko ina.

Pantami
Isa Ali Ibrahim Pantami Hoto: @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

A shekarar 2018 aka kirkiro da wannan lamba a kasar Birtaniya domin a karrama kwararrun masana.

Bayanan da ke shafin yanar gizon wannan kungiya ta Duniya ya nuna Farfesa Isa Ali Ibrahim ne kadai wanda ya fito daga kasar Afrika wanda aka san da zaman shi.

Kara karanta wannan

Osogbo zuwa Legas a kasa: 'Dan Najeriya ya fara tattakin karrama MKO Abiola

Hakan zai kuma ba Ministan dama wajen tantance sababbin wadanda za a ba wannan lambar girma, tare da iya aiki manyan gwamnatoci, kwararru da kungiyoyi.

Karin matsayi a kan matsayi

Isa Pantami ya samu shaidar CIISec ne kusan shekara daya bayan jami’ar fasaha ta tarayya da ke garin Owerri ta kara masa matsayi zuwa cikakken Farfesa a fanninsa.

Wannan karin matsayi da aka yi wa malamin a lokacin da yake aikin Minista ya jawo surutu. Kungiyar ASUU ta malaman jami'an ta nesanta kanta daga matsayin.

Ma'aikaci ya rasa albashi

A makon jiya ne aka samu labari cewa Lauyoyin hukumar ICPC sun yi galaba a kan wani Muhammed Nasiru da suka kai kara a babban kotun jiga na garin Jos.

Hukumar ICPC ta zargi tsohon ma’aikacin da karbar albashi ba tare da ya cancanci mukamin ba. A dalilin haka aka ce ya dawo da albashin da ya rika karba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shigowar Kasaita Da Amarya Amina Isiyaka Rabiu Tayi A Wajen Liyafar Aurenta

Asali: Legit.ng

Online view pixel