Babu Inyamurin da Zai Mulki Najeriya a Zaben 2023, Inji Tsohon Gwamna Orji Kalu

Babu Inyamurin da Zai Mulki Najeriya a Zaben 2023, Inji Tsohon Gwamna Orji Kalu

  • Jigon Jam'iyyar APC, kuma tsohon gwamna a Kudancin Najeriya ya fadi wasu maganganu masu daukar hankali
  • Ya bayyana cewa, sam ba zai yiwu a yanzu wani dan kabilar Inyamurai ya gaji Buhari ba saboda wasu dalilai
  • Peter Obi dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu maso Gabas, yanki mai yawan Inyamurai a Najeriya

Najeriya - Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu a ranar Talata 20 ga watan Satumba ya ce babu wani Inyamuri da zai lashe zaben 2023 mai zuwa, wanda a bayyana ya yi fatan rasa nasarar Peter Obi, PM News ta ruwaito.

Peter Obi, wanda dan takarar shugaban kasa ne a jam'iyyar Labour ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar, kuma yana alfahari da yawan mabiya a Najeriya, musamman a kudancin kasar.

Peter Obi ba zai ci zaben 2023 ba, inji tsohon gwamna a Najeriya
Babu Inyamurin da zai mulki Najeriya a zaben 2023, inji jigon APC | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta kuma ruwaito shi yana cewa, Tinubu ya zama shugaba a Najeriya shi ne alherin Inyamurai.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Duk da cewa bai da wata madafa da tsarin cin nasara, amma ya yi imanin cewa, jama'a masu goyon bayansa ne kashin bayan nasararsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabancin Najeriya ba na kabilanci bane

Kalu ya zanta da manema labarai, ya ce batun shugabancin Najeriya ba na kabilanci bane, kuma a baya ya shawarci jam'iyyun siyasa su mika tikitin shugaban kasa Kudu maso Gabas.

A cewarsa:

"Da suka ki yin hakan, kuma dake batun shugabanci ba na kabilanci bane, haka na hakura. Ban da matsala dan Inyamuri ya zama shugaban kasa. Amma ya kamata mu yi hakan da sauran 'yan Najeriya.
"Idan bamu dama da sauran 'yan Najeriya ba, hakan ba zai haifar da da mai ido ba kuma duk sanuwanka. Shugaba ne na Najeriya ba shugaban yankin Inyamurai ba."

Kalu ya kuma bayyana cewa, ai shi ma Inyamuri ne na gaske, kuma cikakken dan Najeriya, amma da za a zabi wani ya gaji Buhari a zaben 2023 to tabbas shine.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Ya kuma bayyana cewa, duk wanda jam'iyya ya tsayar shi za a zaba.

Ya kara da cewa:

"Na zabi na zama a dan AOC. Me zan sa na zabi Tinubu? Hauka ne kuma ba zan yi hakan ba. Zabe batu ne na millar jam'iyya, ba millar kabilanci ba."

Ya kuma yi kira ga inyamurai da su jira wani lokaci domin su domin kuwa yanzu ba lokacinsu bane.

Lagon Atiku a Kebbi Ya Yi Sako-Sako, Jiga-Jigan PDP da Yawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC

A wani labarin, jam'iyyar APC a jihar Kebbi ya karbi wasu jiga-jigan siyasan da suka sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP, PM News ta ruwaito.

Daya daga jiga-jigan da suka sauya sheka akwai tsohon babban oditan PDP, Alhaji Rabi'u Sa'idu, tsohon sakateren kwamitin riko na PDP Alhaji Sirajo Ibrahim da wasu manyan mambobin PDP 15 daga unguwar Bubuce a karamar hukumar Augie ta jihar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Arewa sun fi karbar Tinubu fiye da Atiku da Kwankwaso, inji jigon APC

Sauran sun hada da Umaru Wakkala, mataimakin shugaban PDP na Bubuce; Salihu Shayi, shugaba matasan yankin; Alhaji Idi Babuce, ma'ajin jam'iyya da kuma Hamza Akilu, oditan jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.