2023: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da PDP Ta Shigar Na Neman Haramtawa Tinubu Da Obi Yin Takara
- Kotu ta yi fatali da karar da jam'iyyar PDP ta shigar na hana Bola Tinubu da Peter Obi shiga zaben shugaban kasa na 2023
- Jam'iyyar hamayyar ta bukaci kotun ta hana Tinubu da Obi shiga zaben saboda sun canja abokan takarar su bayan sun zabi na wucin gadi
- Kotun ta ce karar da PDPn ta shigar ba shi da inganci kuma wani yunkuri ne kawai na bata lokacin kotu don haka ta yi watsi da shi
Abuja - Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar na neman a soke takarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC da Peter Obi na Labour Party, The Cable ta rahoto.
A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1016/2022, PDP ta kallubalanci sauya yan yan takarar mataimakan shugaban kasa da APC da Labour Party suka yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta roki kotun ta tursasawa hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta hana Tinubu da Obi sauya abokan takararsu da Kashim Shettima da Datti Baba Ahmed.
Jam'iyyar ta bukaci kotu ta ayyana takarar Tinubu da Obi a matsayin haramtaciya sai dai idan za su dawo da tsaffin abokan takararsu - Kabiru Masari da Doyin Okupe.
Jam'iyyar ta PDP ta ce dokar zabe na Electoral Act 2022 bai bada damar zaben abokin takara na wucin gadi ba.
Hukuncin kotu kan karar na PDP
Yayin yanke hukunci a ranar Litinin, Mai Shari'a Donatus Okorowo, ya ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar.
Ya ce karar ba ta da 'inganci' kuma wani 'mataki ne na bata lokacin kotu'.
Daga bisani, ya yi watsi da karar.
Da Dumi-Dumi: Fitacciyar Jam'iyyar Najeriya Ta Kori Dan Takarar Shugaban Kasarta Da Wasu Mutum 7 Gabanin Zaben 2023
Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015
A wani rahoton, Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.
Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.
Amma, Wike cikin sanarwar da kakakinsa, Kelvin Ebiri ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana kalaman da aka danganta da Lamido a matsayin abin kyama da raini.
Asali: Legit.ng