Fitacciyar Jam'iyyar Najeriya Ta Kori Dan Takarar Shugaban Kasarta Da Wasu Mutum 7 Gabanin Zaben 2023

Fitacciyar Jam'iyyar Najeriya Ta Kori Dan Takarar Shugaban Kasarta Da Wasu Mutum 7 Gabanin Zaben 2023

  • Akwai yiwuwar jam'iyyar ADC ba za ta tsayar da dan takarar shugaban kasa ba a babban zaben Najeriya na 2023
  • Dumebi Kachikwu ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar kafin shugabannin jam'iyyar suka kore shi
  • Hukumar zabe ta INEC ta rufi lokacin sauya sunan dan takarar shugaban kasa na zaben 2023

Abuja - Kasa da watanni biyar kafin babban zaben shekarar 2023, shugabannin jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, sun kori dan takarar shugaban kasarta, Dumebi Kachikwu, kan zargin cin amanar jam'iyyar, Premium Times ta rahoto.

Legit.ng ta tattaro cewa an kore shi ne makonni bayan biyu bayan wani tsagin jam'iyyar da ke biyayya ga shugaban jam'iyyar na kasa, Ralph Nwosu, sun sanar da dakatar da shi.

Dumebi Kachikwu
Fitacciyar Jam'iyyar Najeriya Ta Kori Dan Takarar Shugaban Kasarta Da Wasu Mutum 7 Gabanin Zaben 2023. Hoto: Dumebi Kachikwu.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Akwai Yiwuwar PDP Za Ta Sha Kaye A Zaben Shugaban Kasa Na 2023, In Ji Jigon PDP Mai Karfin Fada A Ji

A kalla shugabannin jam'iyyar na jihohi 27 da Kachikwu tunda farko sun bukaci a Nwosu ya yi murabus daga kujerarsa da cewa 'ya dade' kan kujerar.

Shugaban ADC ya dade a ofis

Shugaban ya shafe shekaru 17 kan kujerarsa duk da cewa kundin tsarin jam'iyyar ta ce kada shugaba ya wuce shekaru takwas a kujerar.

Amma, jam'iyyar ta ce halin Kachikwu bai dace da wanda ke son zama shugaban kasa ba, saboda sukar kwamitin NWC da Nwosu ke jagoranta.

Jam'iyyar, ta bakin mataimakin shugabanta na kasa (siyasa) Bamidele Ajadi, a baya-bayan nan ta ce:

"NWC ta damu da bidiyon sharri da Mr Kachikwu Dumebi ya yi kuma ya baza a gari, inda ya yi niyyar bata sunan jam'iyya mai son zaman lafiya da kawo cigaba ta African Democratic Congress da shugabanninta."

Kachikwu ya saba dokokin jam'iyya, In Ji Nwosu

Amma cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, 16 ga watan Satumba, Nwosu ya ce kwamitin ladabtarwa mai mutum 7 ta samu Kachikwu da manyan laifuka na cin amanar jam'iyya, saba kudinta da wasu laifukan.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Duk Da Ziyarar Atiku, Makinde Ya Ce Dole Ayu Yayi Murabus

Shugaban jam'iyyar ya ce kwamitin ta zauna sau shida tsakanin 8 zuwa 14 ga watan Satumba don tattauna zargin da ake yi wa dan takarar shugaban kasarta.

"Kwamitin ta samu Mr Dumebi Kachikwu da wasu da laifin da ake zarginsu da shi bisa sashi na 15 na kundin tsarin mulkin jam'iyya an kori Mr Dumebi Kachikwu da sauran daga jam'iyya.
"NWC ta yi taro a ranar 16 ga watan Satumba don tattaunawa kan rahoton kuma ta amince da rahoton sannan ta yi kwaskwarima."

An kori Kachikwu tare da wasu mambobi bakwai, sune shugaban jam'iyya na jihar Kogi, Kingsley Oggah, ciyaman na Edo, Kennedy Odion, Kabiru Hussaini, Alaka William, Bello Isiyaka, Musa Hassan da Clement Ehiator.

Shugabannin jam'iyyar sun ce korar mutane takwas din wani mataki ne na tsaftace jam'iyyar kuma ta bukaci mambobinta su mayar da hankali kan aikin da ke gabansu.

Babban Jam'iyya A Najeriya Ta Dakatar Da Dan Takarar Shugaban Kasarta

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gida: Shugaban PDP ya Mika Mulki ga Mataimakinsa, Ya Bayyana Dalili

Tunda farko, Jam'iyyar African Democratic Congress, ADC ta dakatar da Dumebi Kachikwu, dan takarar shugaban kasarta, The Cable ta rahoto.

Hakan na zuwa ne awanni bayan da Kachikwu ya goyi bayan kiran da ciyamomin jam'iyyar suka yi na cewa Ralph Nwosu, shugaban jam'iyyar na kasa ya yi murabus bayan shekaru 17 a ofis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel