Sanata Ya Budewa Wike da 'Yan PDP Kofa, Ya yi Masu Tayin Shigowa Jam’iyyar APC

Sanata Ya Budewa Wike da 'Yan PDP Kofa, Ya yi Masu Tayin Shigowa Jam’iyyar APC

  • Smart Adeyemi ya fadawa Nyesom Wike da sauran wadanda ake rigima da su a PDP, su dawo APC
  • Sanatan yace saboda ayi adalci, Gwamnonin Arewa suka yarda ‘dan takaran APC ya fito daga Kudu
  • A halin yanzu babu zaman lafiya a jam’iyyar PDP tun da Atiku Abubakar ya zama ‘dan takaran 2023

Abuja - Smart Adeyemi ya yi kira ga Gwamna Nyesom Wike na Ribas da duk wadanda aka fusata a jam’iyya PDP, da su tsallako zuwa APC.

Sanata Smart Adeyemi mai wakiltar yammacin Kogi ya yi wannan kira a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a Abuja kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

‘Dan majalisar yake cewa idan ana maganar jam’iyyar da ke da tunanin talaka, babu irin APC. A halin yanzu da ake shirin zabe, PDP tana cikin rikici.

Kara karanta wannan

Akwai Aiki A gaba: Sanatan PDP Ya Bayyana Abun Da Zai Faru Idan Ayu Ya Yi Murabus

Nyesom Wike da mutanensa sun dage sai an sauke Iyorchia Ayu daga shugabancin jam’iyya. A gefe guda akwai Atiku Abubakar da Dr. Ifeanyi Okowa.

Mun sha bambam da PDP - Adeyemi

Sanata Adeyemi yake cewa saboda a zauna lafiya a Najeriya, shiyasa jam’iyyarsu ta APC ta fito da ‘dan takararta na shugaban kasa daga yankin Kudu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da APC ta ba Bola Tinubu tuta, Atiku Abubakar ne za iyi wa jam’iyyar hamayya ta PDP takara, wanda suke ganin ba ayi wa yankinsu adalci ba.

Nyesom Wike
Nyesom Wike da Gwamnan Legas Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

An rahoto ‘Dan majalisar dattawan yana kira da babbar murya ga duk wadanda suka yi fushi da tafiyar PDP, su sauya-sheka domin a dama da su a kasa.

Gwamnonin Arewa sun cancaci yabo

“Sauran jam’iyya suna cikin matsala domin ba su yarda da hadin-kan Najeriya ba. Ya kamata a yabawa gwamnonin Arewa da suke ce a ba Kudu mulki.”

Kara karanta wannan

Za Muyi Wa Atiku Ritaya, ‘Dan Ci-Ranin Siyasa Ne Daga Dubai Inji Kashim Shettima

“Najeriya na bukatar hadin-kai, adalci, fadada tattalin arziki, kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Wadannan abubuwa ne ake bukata yau a Najeriya.

- Smart Adeyemi

Akwai rikici a APC?

Jam’iyyar APC za ta zauna da wadanda suka nemi takarar shugaban kasa ba suyi nasara ba, akwai isasshen lokacin da za ayi zama da kowa domin a tafi tare.
Akwai sauran watanni biyar a gabanmu kafin a kai ga gudanar da zabe. Kowa yana son ya shigo APC domin ita ce jam’iyyar da ke samun nasara a kasa.

- Smart Adeyemi

Tinubu zai shiga takara

Rahoto ya zo cewa jita-jita na yawo daga bakin mutanen Peter Obi cewa ‘dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu zai hakura da shiga takara a zabe mai zuwa.

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC yace Tinubu nan kalau, da shi za a gwabza a neman takara domin bai cikin rashin lafiya.

Kara karanta wannan

An Shigar da Kara Domin Hana Kwankwaso da Abokin Takararsa Neman Shugaban Kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel