Za Muyi Wa Atiku Ritaya, ‘Dan Ci-Ranin Siyasa Ne Daga Dubai Inji Kashim Shettima

Za Muyi Wa Atiku Ritaya, ‘Dan Ci-Ranin Siyasa Ne Daga Dubai Inji Kashim Shettima

  • Kashim Shettima ya bayyana yadda APC za ta dankara ‘dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kasa a zaben 2023
  • Tinubu ne ya fito da Yemi Osinbajo, Fashola, Lai Mohammed, da Aregbesola, Shettima yace Atiku bai reni kowa ba
  • ‘Dan takarar mataimakin shugaban kasar yace Atiku bai dawowa Najeriya sai kakar zabe, ya yi zamansa a kasar UAE

Abuja - ‘Dan takarar jam'iyyar APC na kujerar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa Atiku Abubakar a zabe mai zuwa da za ayi.

The Nation ta rahoto Kashim Shettima yana mai cika baki a ranar Lahadi, 11 ga watan Satuma 2022, yace su za su yi nasara a zaben shugaban kasa.

Sanata Shettima yake cewa idan kwarewa a aiki, tarihi, iya jagoranci da gina shugabanni ake magana, Atiku ba zai iya karawa da Bola Tinubu ba.

‘Dan siyasar yake cewa tikitin Tinubu/Shettima zai yi wa Atiku Abubakar ritaya a zaben 2023.

Tsohon gwamnan na Borno ya yi wannan bayani ne a lokacin da ‘Yan kungiyar ‘APC National Integrity Movement’ suka kai masa ziyara a garin Abuja.

'Dan ci-ranin siyasa

Rahoton yace Shettima bai tsaya nan ba, ya yi alkawarin idan Bola Tinubu ya karbi mulki, tun a makon farko a ofis zai nada wadanda zai yi aiki da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kashim Shettima
Sanata Kashim Shettima da Bola Tinubu Hoto: Shafin Kashim Shettima @KashimSM
Asali: Twitter

Shettima yake cewa Atiku Abubakar ‘dan ci-rani ne a siyasa, wanda bai dawowa Najeriya daga birnin Dubai sai an fara shirin yin zaben shugaban kasa.

Yayin da Atiku Abubakar ya tare a kasar United Arab Emirates yana shakatawa, Sanata Shettima yace shi da Bola Tinubu sun yi zamansu ne a kasarsu.

Haka zalika ‘dan takaran yace sun gina mutane a gwamnati, shi kuwa Atiku bai raini kowa ba. Shettima yace shi ya fito da irinsu Gwamna Babagana Zulum.

Me Atiku ya yi wa mutane?

Ganin dukkaninsu sun fito daga yankin Arewa maso gabas, tsohon gwamnan na Borno yace duk da Atiku tamkar ubansa ne, amma bai taimaki kowa ba.

“Atiku ba zai iya nuna ayyuka uku da ya kawowa Arewa maso gabas ko Arewacin Najeriya a shekaru takwas da ya yi a mataimakin shugaban kasa.”
“Shin yana ma shiri da tsofaffin gwamnonin Adawa? Nyako da Ngilari duk suna tare da mu.”

Satar kudi a APC

An ji labari Idowu Olaonipekun da Ayinde Suuru sun rubuta takarda mai neman fallasa asirin shugabannin APC na jihar Ogun zuwa ga uwar jam’iyya.

Korafin na Olaonipekun da Suuru yace shugaban jam’iyya da sakatarensa sun dauke kudi daga asusun APC zuwa akawun dinsu, ana zargin an sace N74m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel