APC Ta Yi Magana Kan Lafiyar Bola Tinubu da Yiwuwar Janye Takarar Shugaban Kasa

APC Ta Yi Magana Kan Lafiyar Bola Tinubu da Yiwuwar Janye Takarar Shugaban Kasa

  • Wasu na yada labari cewa Asiwaju Bola Tinubu zai janye takarar neman zama shugaban Najeriya
  • Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya karyata rade-radin
  • Festus Keyamo yace Bola Tinubu yana cikin koshin lafiya, babu abin da za isa ya fasa shiga takara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ya musanya labarin da ake ji na cewa Asiwaju Bola Tinubu zai fasa yin takarar 2023.

Jaridar This Day ta rahoto cewa ana rade-radin Asiwaju Bola Tinubu zai hakura da neman kujerar shugaban kasa saboda bai da isasshen lafiya.

Kwamitin da ke yi wa ‘dan takarar kamfe ya nuna cewa babu kanshin gaskiya a wannan batu.

Mai magana da yawun bakin kwamitin, Festus Keyamo ya fitar da jawabi a ranar Litinin, 12 ga watan Satumba 2022, yana mai martani kan haka.

Kara karanta wannan

Takarar Kujerar Shugabancin Kasa Ta Jawo An Tona Silar Arzikin Bola Tinubu a Duniya

Festus Keyamo yace wannan labari ba gaskiya ba ne domin kuwa Bola Tinubu garau yake, cikin koshin lafiya, kuma zai iya jurewa wahalar kamfe.

'Dan Takarar Shugaban Kasa
Asiwaju Bola Tinubu a Legas Hoto: @OfficialBAT
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Wannan ba komai ba ne illa kanzon kuregensu. ‘Dan takararmu yana da karfi, koshin lafiya, kuma zai iya rungutsumin yakin neman zabe.
‘Yan adawa za su ji da kyau daga gare shi (Bola Tinubu) nan ba da dadewa.”

- Festus Keyamo

An yi wa Peter Obi martani

Jawabin da Keyamo ya fitar, ya yi raddi ga magoya bayan Peter Obi a kafafen sada zumunta da suke cewa ‘dan takaran na APC bai da lafiya sosai.

Kwamitin yakin neman zaben ya fadawa mutanen Obi su guji yada wannan jita-jita idan ba su da abin da za su fada domin tallata ‘dan takaransu.

Premium Times tace Keyamo ya tabo zargin da ake yi wa magoya bayan Tinubu na yin kira ga Yarbawa su guji zaben Peter Obi ya karbi mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Za Muyi Wa Atiku Ritaya, ‘Dan Ci-Ranin Siyasa Ne Daga Dubai Inji Kashim Shettima

An ji ‘dan takarar jam’iyyar LP yana maganar wani sako da ake yadawa a Whatsapp da sunan magoya bayan Tinubu, ana jan-kunnen mutane a kan shi.

Ministan kwadagon yace babu ruwan gwaninsu da wadannan sakonni, kuma ya kalubalanci Obi ya fadawa Duniya inda ya samu sakon a WhatsApp.

Yadda LP za ta ci zabe a 2023

Dazu ku ke jin labari cewa ‘Yan tafiyar Peter Obi sun tsara dabarar doke Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Bola Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.

Magoya Bayan Peter Obi sun yi harin Jihohi biyar domin lashe zaben shugaban Kasa. Wadannan jihohi su ne Legas, Kano, Ribas, Nasarawa, da Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng