NNPP Ta Zabi Tsohon Abokin Tafiyar Buhari Ya Maye Gurbin Shekarau a Takarar Sanata

NNPP Ta Zabi Tsohon Abokin Tafiyar Buhari Ya Maye Gurbin Shekarau a Takarar Sanata

  • Sanata Rufai Hanga ya samu damar komawa majalisar dattawa domin wakiltar tsakiyar Kano a 2023
  • A yau ne Jam’iyyar NNPP ta tabbatar da Rufai Hanga a matsayin ‘dan takaran Sanatan Kano ta tsakiya
  • Hanga ya samu tikiti a jam’iyya mai alamar kayan marmari, shi ne zai maye gurbin Ibrahim Shekarau

Kano - Jam’iyyar hamayya ta NNPP mai alamar kayan marmari, ta tsaida wanda zai yi mata takarar Sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2023.

Ibrahim Adam wanda yana cikin hadiman jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya tabbatar da wannan a shafin Facebook.

Malam Adam ya daura hoton Rufai Hanga a yammacin Alhamis, 8 ga watan Satumba 2022, inda ya yi masa take da cewa ‘Mai girma Sanata’.

Wannan ya yi nuni ga cewa Sanata Rufai Hanga ne wanda jam’iyyar adawa ta NNPP ta ba takaran ‘dan majalisa na yankin tsakiyar Kano.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda ‘Yan APC Suka Wanke Wajen Gangamin Taron PDP a Wata Jahar Arewa

Mun fahimci shugabannin NNPP na tsakiyar Kano sun yi taro a filin wasa na Sani Abacha da ke titin Madobi, inda suka tabbatar da takarar.

Madakin Gini bai yi takara ba

Hanga yana cikin wadanda tun farko aka yi tunani zai samu wannan takara, kafin Sanata Ibrahim Shekarau ya bar APC a watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rufai Hanga
Sanata Rufai Hanga Hoto: @MuhdRH
Asali: Facebook

Sauran wadanda aka yi tunanin za su nemi wannan takara sun hada da tsohon ‘dan majalisar tarayya na Dala, Hon. Aliyu Madakin Gini.

Hadimin Kwankwaso yace Aliyu Madakin Gini bai cikin wadanda suka nemi tikitin, zai cigaba da yin takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya.

Wanene Rufai Hanga?

Rufai Hanga ya rike kujerar Sanata mai wakiltar bangaren Kano ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin shekarar 2003 zuwa Mayun 2007.

Baya ga haka shi ne shugaban farko na jam’iyyar Congress for Progressive Change. Daga baya CPC tana cikin wadanda suka narke a cikin APC

Kara karanta wannan

Kwankwaso @66: Wasu abubuwa 10 da ba ka sani ba a game da ‘Dan Takaran NNPP

Hanga yana cikin na hannun daman Muhammadu Buhari tun a ANPP. A karshen shekarar bara aka ji ya bada sanarwar sauya-sheka daga APC.

Rufai Hanga zai canji Shekarau

Legit.ng Hausa ta fahimci hakan ya zo ne bayan Sanata mai-ci Ibrahim Shekarau ya canza sheka daga jam’iyyar, ya koma PDP a karshen watan Agusta.

Kun ji labari cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin abin da ya jawo Ibrahim Shekarau ya bar NNPP bayan watanni uku kacal ‘a jam'iyyar.

'Dan takarar shugaban kasar kuma tsohon Gwamnan Kano yace rashin isasshen lokaci ya sa Shekarau ke korafin ba ayi adalci wajen yin kaso ba.

A dokar zabe, NNPP tana da kwanaki 14 ta gabatarwa hukumar INEC sunan sabon ‘dan takara a dalilin rasa wanda aka tsaida da farko ko idan ya mutu.

NNPP za ta ci zabe a 2023

Da muka tuntubi Saifullahi Hassan, wanda yana cikin Hadiman da ke taimakawa Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna mana suna hangen nasara a 2023.

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya Ya Jawo Aka Gaggauta Fita da Atiku Kasar Waje - 'Dan Kwamitin Zaben APC

Saifullahi Hassan ya nuna ficewar Ibrahim Shekarau ba za ta hana su kai labari a jihar Kano ba, bugu da kari, yace suna fatan lashe babban zabe na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel