Tsohon Hadimin Buhari Ya Shigo Takarar Gwamnan Kano Gadan-Gadan Daga Baya
- Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada zai yi takarar Gwamna a karkashin jam’iyyar adawa ta ADP mai alamar littafi
- ‘Dan majalisar na Birnin Kano ya fice daga APC bayan dogon lokacin ana samun sabani, ya samu takara a ADP
- Sha’aban Ibrahim Sharada zai gwabza da Nasiru Gawuna, Abba Kabir Yusuf, Sadiq Wali da wasu ‘yan takara a 2023
Kano - Tsohon Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya fito takarar gwamna a jam’iyyar ADP.
Rahoton Daily Trust yace Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya shaidawa mutanen Kano burinsa da ya ayyana niyyar neman Gwamna
An yi wani taro a cibiyar matasa ta Sani Abacha Youth a Kano a ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba 2022, inda ‘dan takaran ya nuna ga gaske yake yi.
Legit.ng Hausa ta fahimci mutane da-dama a Kano sun samu halartar taron da Sharada ya kira.
Dauda Kahutu Rarara yayi wasa a wajen taron, ya kuma gabatar da wasu ‘yan takarar ADP irinsu Aminu Ladan Abubukar da Adam Abdullahi Adam.
Tirka-tirka a jam’iyyar ADP
Legit.ng Hausa ta fahimci wannan na zuwa ne a lokacin da Nasiru Koguna yake ikirarin shi ne asalin ‘dan takaran ADP a zaben Kano ba Sharada ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A zaben fitar da gwani da aka yi a watan Yuni, Koguna aka sanar a matsayin ‘dan takaran jam’iyyar ADP, amma sai daga baya ne maganar ta canza.
Shugabannin jam’iyyar ta ADP mai alamar littafi sun ce Hon. Sharada ne ‘dan takara a 2023.
Siyasar Kano a 2023
Hon. Sharada zai nemi takarar gwamnan jihar Kano ne a karkashin jam’iyyar hamayya ta Action Democratic Party (ADP), bayan ya fice daga APC.
A halin yanzu jam’iyyar APC ta tsaida Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo, mataimakan gwamna mai-ci da tsohon kwamishina a jihar Kano.
An ji labari PDP ta ba Sadiq Wali da Yusuf Bello Dambatta takara, dukkaninsu sun rike kwamishononi a gwamnatin Ganduje da kuma na Kwankwaso.
Ku na da labari jam’iyyar NNPP kuwa ta tsaida Abba Kabir Yusuf da Aminu Abdussalam Gwarzo ne, wadanda suka yi takara a PDP a zaben 2019.
Tsohon kwamishina kuma jigo a APC, Bala Gwagwarwa shi ne wanda zai yi takarar gwamna a SDP, yayin da Salihu Tanko Yakasai yake yin takara a PRP.
Asali: Legit.ng