Mataimakin Shugaban PDP Ya Fice Daga Jam’iyya, Ya Aikawa Iyochia Ayu Wasikarsa
- Ana tsakiyar rigimar cikin gida sai aka ji sanarwar Hon. Leye Odunjo na ficewa daga jam’iyyar hamayya ta PDP
- Leye Odunjo shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a jihar Ogun, kuma ‘dan siyasa wanda ake ji da shi sosai
- Kafin zamansa shugaba a PDP, sai da Odunjo ya yi shekaru takwas a matsayin ‘dan majalisar dokoki na jihohi
Ogun - Dazu nan muka samu labari Hon. Leye Odunjo ya sauka daga matsayinsa na mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na reshen jihar Ogun.
The Nation ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba 2022, tace Hon. Leye Odunjo ya bada sanarwar ficewarsa daga jam’iyyar PDP.
Tsohon ‘dan majalisar ya shaidawa Duniya ya yi murabus ne a wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu.
A wannan takarda da ta fita daga Sikirulai Ogundele, mataimakin na sa ya sanar da uwar jam’iyya cewa ya ajiye mukaminsa, ya kuma fita daga PDP.
‘Dan siyasar ya fadawa Sikirulai Ogundele cewa ya bar PDP ne saboda ra’ayin kansa, ya kuma shaida cewa ya yi matukar jin dadin aiki da mutanenta.
Ficewar za ta girgiza PDP a Ogun
Wannan fitaccen ‘dan siyasa wanda ya fito daga Ado-Odo/Ota ya rubuta a takardar da ya aikawa shugabannin PDP cewa zai yi kewansu tun da ya bar su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shi kan shi ‘dan siyasar yace ficewarsa daga PDP inda aka san shi, za ta ba mutane mamaki. Odunjo ya gode da irin zaman mutuncin da aka yi a SWC.
Jam'iyya ta rasa 'Dan amana
Daily Post tace tun 1999 Odunjo yake tare da jam’iyyar hamayyar, kuma ya rike mukamai sosai.
A tsawon shekarun da ya yi, ‘dan siyasar ya zama shugaban jam’iyya na yammacin Ogun, ya kuma taba zama mukaddashin shugaban PDP a jihar.
Baya ga mukamai, Odunjo ya yi takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya, ya nemi kujerar gwamna, a zaben 2019 ya shiga takarar majalisar dattawa.
Rahotanni sun ce da alama tsohon ‘dan majalisar zai sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, zai taimakawa Dapo Abiodun da Bola Tinubu a 2023.
N2bn sun yi kafa daf da zabe
An ji labari kimanin Naira biliyan 11.9 ake zargin sun bace daga asusun jihar Kwara tsakanin 2011 da 2019. Premium Times ta fitar da wannan rahoto.
Wani binciken kudi da aka yi, ya bankado yadda aka cire N2bn daga asusun gwamnatin Kwara, an yi wannan ta'asa ne a lokacin zaben 2019.
Asali: Legit.ng