Ango Abdullahi: Manyan Arewa Sun Fadi ‘Yan takaran da Babu Ruwansu da su a 2023

Ango Abdullahi: Manyan Arewa Sun Fadi ‘Yan takaran da Babu Ruwansu da su a 2023

  • Farfesa Ango Abdullahi ya shaidawa Duniya cewa mutanen Arewa ba su tsaida wani ‘dan takara tilo a zaben 2023 ba
  • Shugaban kungiyar ta NEF ya halarci bikin kaddamar da littafi, ya yi bayanin matsayinsu a matsayin dattijon Arewa
  • Ango Abdullahi ya yi tir da yadda ake neman cin zabe ta hanyar raba kan jama’a, yace ba za su goyi bayan wannan ba

Kaduna - Shugaban kungiyar nan ta Northern Elders Forum (NEF) ta dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi yace Arewa ba ta da wani ‘dan takara a 2023.

Vanguard ta rahoto Farfesa Ango Abdullahi yana cewa yanzu mutanen yankin Arewa sun yi hankali, ba za su bi bayan wani ‘dan siyasa a zabe mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

Shugabar Hukumar NIDCOM Ta Cire Rigar Mutunci, Ta Dirkawa Wani Zagi a Twitter

Da yake bayani wajen bikin kaddamar da wani littafi a garin Kaduna, Farfesan yace babu ruwan mutanensa da ‘dan takaran da ke neman raba kan mutanen Arewa.

“Arewa za ta shiga duk wani harkar siyasa da zabe kamar sauran yankuna, tare da girmama duk wadanda suka girmama mu.
Arewa tana son shugabannin da za su yi jagoranci da gaskiya, kwarewa, tausayi da tsoron Allah."

- Ango Abdullahi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba mu tare da masu kawo sabani

“Ba za mu goyi bayan wani ‘dan takara da ba zai iya yi mana bayanin yadda zai kawo gyara a shugabanci da kuma nagartar shugabanni ba.
Na biyu kuma shi ne ba za a tilastawa mutanen Arewa daukar shawarar da ba za ta canza su daga irin yanayin da suke ciki a halin yanzu ba."

- Ango Abdullahi

Arewa
Buhari da Manyan Sarakunan Arewa Hoto: newswirengr.com
Asali: UGC

A rahoton Daily Trust, Farfesan yace a yankin na Arewa ake fama da matsalar tsaro da kuma tabarbarewar arzikin da ya shafi Musulmi da Kirista.

Kara karanta wannan

Tsohon Na Hannun Daman Kwankwaso Ya ki Yarda Ya yi Aiki a Kwamitin Kamfen Peter Obi

A dalilin haka tsohon shugaban jami’ar ta ABU Zariya ya yi Allah-wadai da masu yin kamfe da sunan addini domin raba kan mutanen yankin Arewa.

Wanda ya san ciwonmu za mu zaba - NEF

“Muna ganin ana yin mafi munin kamfe mara amfani domin a raba kan Hausa da Fulani, kuma a jawo sabani tsakanin Kiristoci da Musulman da ke Arewa."

- Ango Abdullahi

Ango Abdullahi yace yanzu mutane sun farga, za su zabi wanda ya san su, kuma zai iya magance matsalolinsu ne."

Shugaban na NEF ya yi amfani da damar, yace babu ‘dan takaran da suke goyon-baya. Hakeem Baba Ahmed yace sabbabbin shugabanni ake bukata a 2023.

Sai Peter Obi ya dage

An ji labari Dr. Kayode Ajulo ya fadawa Peter Obi cewa kafofin sada zumunta suna da amfani wajen nuna shahara, amma ba da su ake zama shugaban kasa ba.

‘Dan siyasar ya nunawa Peter Obi mai takara a LP ya yi amfani da barakar da ke cikin PDP, ya bi kungiyoyin ma’aikata, kuma ya hada-kai da manyan Najeriya.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng